Kyalkyalin Kauna 7

 EPISODE 7️⃣









Wuraren 3:30 daidai tafito daga shagon Maman Intee tana kalle kallen dan wajen gaban shagon dababu wani mota yanzu datafito ko kadan bataji komi ba keke data gani yazo zai wuce ta tare da sauri ta hanyar daga mishi hannu tashiga suka wuce radio Keken duk yacika mata kunne damai keken ya kunna, muryan Baba taji a radio kaman daga sama yana jawabi kaman jawabin dayayi ne bayan karin girman da akamai.


“Inama alumman mutanen nigeria gabaki daya alkawari cewa zanyi yaki da rashin gaskiya, zan kawo karshen barayi da yan shaye shaye, zan kawo karshen karban cin hanci da rashawa da akafi sanin polisawa da halin, zan kawo karshen miyagun abubuwa sannan zan tabbatar da tsaro da kuma gaskiya…..” wani kalan cute smile tasaki dayasa tai kaman wata Barbie doll sabida kyau tanajin wani irin farin ciki azuciyanta tana alfahari da Baba irin sosai din nan. 

Har gaban gidansu Mai keken yakawota bayanshi tayi sanan tajuyo ganin motan Baba yasa tagane yana gida, ahankali tabude gate tashiga ciki da sallama su Nanah ne da Sa’a dakuma Farida ke tsakar gida kan tabarma ga abubuwa daban daban agabansu harda takalma suna gwadawa dasauri tayi cikin gidan Nanah naganinta tasaki takalminta taruga aguje ta rungumeta cikeda tsananin so dakuma shakewa tace “oyoyo Anty Yasmeen kinga Baba yasayo mana abubuwa da yawa naki nadaki wajen Ammi, itane tarike naki, nima kinga yasaya mini takalmin kwas kwas” wani kalan murmushi Yasmeen tayi tareda gyarama Nana kitson kalaban dake kanta dake lilo yana neman shiga idanunta tace “dagaske, sakeni kiga naje na amsa nima naga nawa takalmin kwas kwas din” tawuce ciki batare daya tsaya kallon nasu Farida ba, da sallama tashiga dakin Ammi, Ammi da Baba nazaune kan kujera suna magana akunyace tace “Baba sannu da zuwa” Ammi tace “sannu da zuwa, zo ga naki takalmin da hijabi da jakan Baban ku yasayo muku” dasauri takarasa gaban Ammi takarbi nata dasune suka rage a leda tana murmushi sosai sabida yanda taji dadi tace “Baba nagode Allah saka da alkhairi” juyawa tayi dasauri zata fita danta kosa taje itama tazauna kusadasu Farida tabude nata tagani kaman daga sama Baba yace “zonan” juyowa tayi da sauri tana zaro manyan idanunta masu shegen kyau da grayish kwallan idanun dake gareta, wani leda Baba yaciro daga jakan aikinshi daga ita har Ammi suka bishi da kallo dan itama Ammi batasan me aledan ba mikamata yar ledan yayi ahankali ta tsugunna ta ijiye ledan kayanta akasa sannan takarasa wajen da Baba kezaune tasa hannunta ahankali takarbi ledan jin kwaline Mai tauri tauri yasa Ammi tace “menene aciki bude mugani” kaman dama jira take Ammi tace haka dawani kalan sauri tabude ledan ganin kwalin waya na techno spark 3 yasa batasan lokacin datawani kalan kurma ihu ba tai wani uban tsalle su Farida suka shigo dagudu dan sun dauka bugunta Baba yayi, cikeda murna tace “Ammi waya, touch screen” saikuma kawai tafada jikin Ammi tafashe da kuka sosai ba kakkautawa, Ammi dariya ma abin yabata tace “kagamini shirme menene nakuka kuma, kaga kuka take Baban Nanah” juyoda kanshi Baba yayi yakalleta yanda tadaura kanta ajikin Ammi tana kuka yace “mena kuka kona karbi wayar ne”? girgiza kai tayi ahankali tana ciro kanta daga jikin Ammi takai hannunta tagoge fuskanta tass, takalli fuskan Baba dake kallonta kur batare daya kyafta idanu ba ahankali tace “Baba nagode sosai” murmushi yayi kawai tareda dauke kai, Ammi tace “tashi kije kisa a chaji, kasamata sim dinta aciki ne?” Ammi ta tambayi Baba dan karaman wayanta na hannunshi daya karba jiya, Gyadamata kai yayi hakan yasa Ammi tai murmushi sosai tace “imaza jekisa chaji to tunda ga nefa saiku shirya islamiyya kan ki dawo wayan tacika dam” murmushi tayi ta tashi tafito su Farida biyeda ita suka shiga dakin nan fa suka shiga tattaba wayan saida sukaji gyaran muryan Baba arude sukasa wayan achaji kowa yamike yashiga shirin islamiyya kafin suyi salla suwuce.



Sai bayan la’asar daya shigo gida Ammi tafito daga kitchen tazo tasameshi zaune akan gado a uwardaka yana kokarin boye bindigarshi akarkashin gado wanda daman anan yake boyewa sabida yara, ahankali tazauna kusadashi anatse tace “Baban Nanah yau ka kashe kudi dayawa, nadauka kudin da aka bakan nan na karin girma fili xaka saya muyi gini” girgixamata kai yayi yace “bazan taba barin gidan nan ba wannan gidan gidan gado ne, iyayenmu suka barmana, saidai nai gyaran gidan amman ba barinshi ba” shiru Ammi tayi hakan yasa Baba yace “gobe ki sayo musu atampopi da kudin dana baki da packet na audugan ku (pad)” gyadamai kai tayi tace “shikenan” yunkurawa tayi zata mike karaf yariketa zaro idanu tayi tana kallonshi tace “Haba babban Nanah, matan gidan nan duk suna nan fa, zan koma kitchen ne mucigaba da girki” murya chan kasa yace “nikuma bukatan ki nake su karasa girkin” bai kara bari tai wani magana ba yasata akan gado.

Sunyi nisa sosai wayanshi na office yahau ringing, dan yanada normal waya na gida yanada waya na office wanda department nasu ne yabasu, ganin baya hayyacinshi yasa da kyar Ammi tace “ana kiran wayanka na aiki” kasa magana yayi ya kankameta yana kara sauri kafin chan yasaki kara sannan yakoma gefenta ya kwanta yana maida ijiyan zuciya yajanyo Ammi yadaurata akan kirjinshi yana shafa bayanta, da kyar ya iya mika hannu yadauki wayan yakai kunnenshi yace “speak” wani kalan yunkurawa yayi yatashi zaune harsaida Ammi ta firgita, yace “awajen wa kaji this information Aliyu”? Shiru yayi saikuma chan yamike tsaye yace “wat I want you to do now is trace the number dayay message din I believe is a whistle blower, but kayi komi lowkey dan most of our people anan station yariga yasayesu you will see me in the next 30mins” katse wayan yayi yajefar yawani kalan diro daga kan gado zaiyi bayi dasauri Ammi ta tashi zaune tace “meke faruwa”? Juyowa yayi yakalleta dan murmushi yayi yace “is work related” hmmm ajiyan zuciya ta sauke bata cika saka sa ido aharkan aikinshi ba but wannan dataji yana gayama Aliyu kada wani yasani she is worried, Aliyu yaronshi ne da dadewa, juyawa Baba yayi harzai shiga bayi Ammi tarikemai hannu tace “Baban Nanah I am worried and I don’t know why? I feel kaman you are about to get yourself in trouble” dan dariya Baba yayi kadan tace “why are you worried normal aikin dana saba zanyi, munsami wani tip kan Pablo Escobar ne da hakan zaisa komashi waye ya bayyana agareni nadade ina neman gayen nan and finally I think lokaci yayi da dubun shi zai cika, inamai tabbatar miki saina kawo karshenshi da karshen business na kwayoyin dayakeyi kodako su uban waye da waye ke bayanshi Alhamdulillah yanzu nazama CP I have my own power and I have my team now, yanzu dai barni nai wanka ana jirana” ahankali Ammi tasakeshi yawuce bayi itakuma tadawo bakin gado tazauna tana shafa kirjinta dataji yana bugawa sosai, bayau Baba yafara aikin police ba infact a police dinshi ma ta aureshi, yasha kama criminals dasuwaye da waye but hakanan yau yana amsa wayan nan taji kawai gabanta nafaduwa and she is not just at ease. Lumshe idanu tayi ahankali tace “Ya Allah ka kare kakuma tsaremini Ibrahim duk inda zaije duk inda kuma zai shiga dan Ibrahim is very very stubborn” ajiyan zuciya tasauke daidai yafito hakan yasa yace “jeki wanka kema” gyadamai kai tayi tashiga bayin kofin tafito harya gama shiryawa riga da wando yasaka na jeans ba uniform ba, bindigarshi yaciro daga kasan bed yabude yaduba bullet kafin ya maida yasake abayan wandonshi sannan yadauki car key nashi da wayoyinshi yakalli Ammi daketa kallonshi yace “natafi pray for me, nakama mutumin nan gwamnati ina mai tabbatar miki saita karamin girma, bye wifey yaran nan makesure sunci abinci sunyi salla kafin su bacci” gyadamai kai tayi tana binshi da idanu ganin kaman she is worried yasa yazo gabanta fuskanta yakama ya manna mata kiss agoshi ahankali yace “please cheer up kada kisamini damuwa dan as it is I am so very happy yanzu you have no idea what kama Pablo means to me and to the entire nation, yaran al’umma zasu rage shaye shaye that is in ma basu daina ba, are you not happy? This is good news” murmushin yake Ammi tamai tace “eh” kumatunta yashafa yace “bye ba lallai nadawo ba maybe gobe zaku ganni” baijira abinda zatace ba yawuce yafita dasauri sauri.

✨KYALKYALIN KAUNA✨



     ✍🏻M SHAKUR

No comments