Kyalkyalin Kauna 4

 EPISODE 4️⃣









Around 4:30 na asuba tabude idanunta tana kallon saman dakinsu kafin ahankali takaranto addu’an tashi daga bacci, kallon yanda Nanah ta cukuikuyeta tayi taredayin murmushi sannan gently tarabata da jikinta ta tashi zaune tana kallon Farida da Sa’a dahar munshari sukeja, lallabawa tayi tasauka daga gadon nasu ahankali wucewa tayi tabude kofan dakinsu ahankali tafito tsakar gidan wucewa tayi bayi dan ko’ina akwai wuta tayo tsarki tafito tadauro alwala tadawo daki ta shimfida dadduma tahau kai tayi sallan isha’i sannan ta tashi tadauko jakan school nata handouts nata taciro tabude babu randa bata karatu aduniya da safe amman bata ganewa dukta yanda zaka mata bata ganewa sannan karanta abu na bata wahala bakowani word ta iya karantawa ba ko rubutawa dudda Islamic studies take abubuwan da ake musu wasu ta sansu a islamiyya but she can’t still write it down, wani zubin fa zatai karatu, zata haddace sannan tazo ta haddace spelling din, amman abu kadan ne zai faru yasa ta manta tass ga FCE dinsu course daya arabashi kusan gida bakwai har gwara datana nursing ma mutum daya na daukan course daya bataso akoreta a FCE, batasan yaya zata kalli Baba ba dudda bai taba fushi dan akorota a school ba kokuma dan batai kokari ba amman tasan babu dadi itane lesson teacher menene menene babu abinda baya daukomata, yanzu haka akwai wata lecturer daya biya a FCE duk ranan Friday take zuwa 4 zuwa 5:30 take mata karatu tana kara koyamata abubuwan da aka musu amman still bata ganewa kota gane mantawa take sai kuma karatu na bata wuta, wani zubin tasan abu but spelling da rubuta abun down kesa tafadi dudda harda spelling lecturer ke koya mata, kuma Sa’a da Farida ma suna koyamata wani zubin ma suke karanta mata handout dinta.

Ajiyan zuciya ta sauke tabude page 10 a handout din na Islamiclaw tafara karantawa tanasa yatsu kaman mai koyan ABCD bill hakki take hadawa take karantawa tayi nisa akaratun kojin bude kofan Baba batayi ba, Baba yadade tsaye bakin kofan yana kallonta kana ganin yanda take karantun kasan she wants to learn it at all cost amman yana bata wuya, babu kalan means da addu’a da basu mata kawai saurin iya abu da ilimin boko ne kawai Allah bai bata ba dudda abin na damun Baba amman bai wani damuba sabida a islamiyya she’s doing very okay dudda nan ma su Farida sun fita ilimi amman still ta iya, ta iya karatun Al Qur’ani ta iya hada baki kawai she is naturally a slow learner, idan Farida da Sa’a zasu iya sura daya a rana daya ita zata iya suran arana biyu ko biyu da rabi saisa ko a Islamiyya ma Farida kanwarta tafita aji.


Dan gyaran murya Baba yayi hakan yasa firgigit tadago kanta tareda ijiye handout din agefe tace “Baba ina kwana” dan murmushi yamata yace “kin tashi kinyi sallan isha’i”? Gyadamai kai tayi da sauri, jinjina kai yayi yace “tashi su Sa’adatu kuyi sallan asubahi to” tashi tayi dagakan dadduman tace “too Baba” shikuma Baba yafice shida su Baffa suka fita daga gidan dan zuwa masallaci.

Salla sukayi sannan kowa ya dauki Al Qur’ani suka shiga karantawa kafin gari yay haske suka fiffito dan zuwa kitchen taya iyayensu aiki, Yasmeen Ammi takalla data gaida tana kallon wani katon pimple guda daya rak daya fito mata atsakiyan goshi tace “zonan” zuwa wajen Ammi tayi dasauri tana murmushi dake bayyana white teeth nata, Ammi dake kallon fuskanta tace “kagan mini shirmammiyan yarinya” Hajjo dake zuzzuba koko akufunan da suka kakkawo tace “hala yau ta tashi da shirmen yan farin ne”? Turo baki Yasmeen tayi ashagwabe tace “Ammi kinga Mama Hajjo ko” murmushi Ammi tayi tana taba pimple din tace “yau idan zaki shagon Maman Intee kidauki pad ki saka ajaka kinajina”? Gyadama Ammi kai tayi akunyace tadan juyo takalli su Hajjo ganin hankalinsu baya kansu yasa takalli Ammi cikin sassayar zakakkiyar yar muryanta  tace “Ammi kinada bread ni banson Kokon nan da kosai” tai maganan tana yatsine fuska dan koko bacci yake sata bana wasaba, murmushi Ammi tayi tace “je inada shi ki dauka saiki maza kiyi wanka Babanki ya saukeki a shagon Maman Intee kinsan yau za’amai karin girma kada ku sashi latti” cikeda murna Yasmeen tace “karin girma Ammi”? Ammi tace “ohh uwar bacci natuna jiya dayana fadi kinyi nisa a jam’iyanna naki” kyalkyacewa da dariya tayi kana ganin yanda yake kasan tana bala’in son Mamanta  hararanta Ammi tayi tace “za’amaida Babanki CP saiki tayashi da addu’a kina dariya awajen” tsalle tayi tace “Alhamdulillah naji dadi Allah taya Baba riko” cikeda farinciki tafito daga kitchen din tawuce falon Maman su inda Baba yake zaune yana duba jarida sallaman ta yasa yadago kanshi yakalleta hakan yasa takarasa wajen kujeran dayake tsugunnawa tayi adan kunyace tace “Baba Allah sanya alheri” murmushi yamata tareda maida kanshi kan jaridan dayake hannunshi itakuma tawuce tadauki bread din da Ammi tasa tazo tadauka, bin bread din Baba yayi da kallo ahankali yace “zai isheki”? Gyadamai kai tayi dasauri tace “eh Baba” wucewa tayi tafito daga dakin zuwa dakinsu inda taga Sa’a da Farida nashan koko da kosai da aka soya, zama tayi gefen Sa’a dake watsa mata harara saikuma kaman wacce ta tuna wani abu tace “Yasmeen kinsan Fahad yace yau zamu hadu narasa a ina zance muhadu wlh tsoron Baba nake” zaro idanu daga Farida har Yasmeeen sukayi suna kallonta, da sauri Yasmeen dan ita bata kaunar fada ko masifan Baba saisa har tsoro take tayi laifi tace “nidai baruwana kema kinsan Baba yahana muyi tadi bayace idan wani nasonka kace yazo gida ba” wani kalan mugun harara Sa’a tamata tace “ni saisa wlh nafison Farida dudda she’s just 15 amman tafiki hankali da mutunci da rufama yar uwanta asiri, sokike Fahad yazo Baba yakoramini shi yaro dan masu kudi Baban ku daya iya firgita mutane Allah yasawake wlh ko zan bari yazo yaga su Baba saina tabbatar yagama fadawa soyayyata yanda kome Baba zaimai ba gudu baja da baya shidai yanasona” tai shiru sannan takalli Farida dake kallonsu tace “Farida kinji bani shawara” kaman jira Farida take dan ita arayuwan ta tanason taji ana hira da zancen samari dasauri tace “ba yau za’ama Baba karin girma ba, bazai dawo da wuri ba, kibari yazo amman saiku tsaya tabayan layi ko Anty Yasmeen”? Dasauri Yasmeen takalli kanta saikuma ta nuna kanta ita hiran kadaima tsoro yake bata tace “ni”? Akufule Sa’a tace “a’a bakeba da gatari ake magana, kinga Farida kada ki kara sata a zancen mu ita ta sani tsoron Baba saiyasa kin kasa auruwa saisa har yau ko me babur baitaba cewa yana sonki ba” adan tsorace Farida dake kallon Yasmeen itama tace “kuma Anty Yasmeen duk kin fimu kyau wlh haka har yan unguwa ke cewa, wani kalan sweet skin gareki coffee coffee, butter butter dake” hararanta Yasmeen tayi ta tashi batare datace musu komiba tashiga cire kaya ta daura zani tafice wanka taje tayo sannan tadawo, gaban sip nasu taje taciro wata atampa mai kyau brown da aka mata dinkin doguwan riga saka sannan tadauki jakan zuwa aiki school nasu tadawo wajensu tazauna handout taciro tamikama Sa’a tace “dan Allah karanta mini page 10 Ya Sa’a mutumin yace shi baya fadin ranan test kuma kinga gobe Friday zani school” fizge handout din Sa’a tayi tace “ni kinaso na taimakeki amman ke baki taimako na” dan murmushi tayi daya karamata wani kalan kyau tace “to kiyakuri bazan karaba, ba Farida tace yazo bayan layi ba, ita saita miki gadi koda Baba yazo saita miki flashing koda wayan Mama ne” sai alokacin Sa’a tai murmushi sannan tabude page 10 din tashiga karanta mata tai shiru tana saurare anatse, daidai Sa’a tazo wani gaba da sauri Yasmeen tace “Ya Sa’a yimin spelling phe……ri…” dasauri Sa’a tace “peripherals wai?” Gyadamata kai Yasmeen tayi da sauri tana ciro wani byro daga jakanta, Sa’a tace “P, e, r, i,p,h,e,r,a,l,s” palm nata Yasmeen ta kalla data rubuta words din ahankali tashiga maimaitawa da baki kafin takulle idanu tana kokarin karanto spelling din. “P, E R E P E” ahankali Farida dake kallonta tace “P, H ne Anty Yasmeen kafin E din” ahankali Yasmeen tabude idanunta takalli tafin hannunta, ajiyan zuciya tasauke dayasa Farida taji idanunta sun kawo kwalla tashi tayi dasauri takwashi cups na kokon dasukasha kawai tafito daga dakin, Yasmeen nabata tausayi tun tana yarinya tana yar karama lokacin tana ganin yanda Ammi ke bugun Yasmeen idan ana koyamata homework agama fada mata ta manta har Ammi tagaji tadena dukanta, gashi Anty Yasmeen tun tana yarinya lokacin yarinya ce mai zuciyan so takoya babu wurin wanda bata zuwa agidan nan yakoya mata karatu but still, su Baba, su Baffa su yayinsu, hatta su Yaya da bama suyi makaranta ba suma sun koyar da Yasmeen ABCD but still, Yasmeen bata taba cewa sabida ta girmeta baratazo takoya mata ba, har yau so da dama zatazo tasameta tabata handout takaranta mata, yanda Yasmeen ke wahala da karatu abin na mata gwarama tadaina makarantan to dole ne karatun bayahuden gwara tacigaba da zuwa wajen Maman Intee koyan girke girke da Islamiyya abinta wannan bokon ba dole dan bakar wahala kawai Anty Yasmeen kesha. Wasu hawaye masu zafi guda biyu ta goge kafin ahankali tadauke bucket din tawuce bayi.



Kusan sau uku Sa’a takaranta mata page 10 din kafin tabata handout din tace “to hada bakin ki karanta naji, kinga kun kusan fara first semester exam gashi bakince malamai kusan 4 ke muku course din ba kuma kowanne da nashi Yasmeen yaya zakiyi wannan na mutum dayane cikinsu yanzu kike page 10, wannan page 10 din nan kadai zai iya daukanki 10days kafin ki gama iyawa ki gama gane spelling da komi wai karatun nan dole ne, ki hakura ki barshi, karatu is not for u Allah bai baki kwakwalwan bane ba kawai, ki sami Baba ki sanar dashi kada kiji tsoro wlh” mayun gray eyes nata Yasmeen tazuba ma Sa’a tanajin wani abu nataso mata daurewa tayi ahankali tace “nidai in karanta kiji mini”? Ijiyan zuciya Sa’a tasauke zuciyanta namata badadi sabida yanda taga Yasmeen na wahala da karatu tace “karanta naji to tunda ke Allah yamiki bakin zurfin ciki” anatse Yasmeen tafara karatun, yanda take hada words da kyar tana fadi zaka dauka yar primary 1 ce, layi biyu tayi masu kyau takakare at the 3rd line wajen kalman Jahillya period, tashi Sa’a kawai tayi tace “nima zanje nai wanka inada lectures 11 gwarake Baban ki yanzu zai wuce dake ya kaiki ni saidai nahau mota, better think about abinda nafada miki and meet Baba da maganan” binta da kallo Yasmeen tayi harta fice daga dakin kafin ahankali tadawo da kanta takalli littafin idanunta kan kalman data kasa fadi, yatsanta tadaura kan Ja din ahankali tace “ga…..no ja is JAAAA” tai shiru tana kallon Hi tace “Hi, kaman hi din hello kenan yauwa ai nasan hi” shiru tayi tana kallon LI, itafa duk words dazata gani ta iya karantawa to tazauna ta haddace spelling din ne tasan yanda ake kiran word din, irin su Apple, cup, house, happy, da sauran kalamai da makaranta yasa ta zauna ta koyi spelling din ta haddace other than that ko she yanzu karubuta mata inhar bata taba zama da takoyi kalman ta iya shi ba to kafin ta iya pronouncing she din nan aiki ne babba agareta.

Labulen dakin aka daga hakan yasa tajuyo dasauri Baba ne yayi wani irin kyau yasa goggagun uniform, yana kallonta yace “da hijabi mutafi” gyadamai kai tayi tamike tawuce sip wani pink gogaggen hijabi tadauka tasaka dake kaimata har kasa tadauki jakan zuwa aiki da flat takalminta najiya tasaka sanan tafito, su Ammi dake tsakar gida sukace “adawo lafiya” gyadamusu kai tayi Nana tabiyota har gate tace “Anty Yasmeen yauma ki kara kawomini tsaraba” wani kalan murmushi Yasmeen tayi sannan ta duko hancinta taja tace “Nanani na ta iya kwadayi ko shikenan zan kawomiki” washe baki Nana tayi tana tsalle tareda mata bye bye ta kwala ihu tace “Baba bye bye” bye Baba yamata yana murmushi shima.


Har gaban shagon Maman Intee ya ijiyeta sannan yaciro 1k a aljihun shi yabata yace “gashi idan kin tashi kikaga babu keke ki koma ki zauna call me da wayan Maman Intee zanzo na daukeki kada ki kara takowa daganan har gida is risky kinji” gyadamai kai tayi ahankali tace “to Baba” tasa hannu zata bude kofar kaman daga sama taji Baba yace “me da me kuke bukata”? Dasauri tajuyo ta kalleshi tana zaro manyan fararen idanunta masu bala’in kyau, maimaita tambayan Baba yayi yace “medame kuke bukata keda yan uwanki”? Ahankali tace “ai Baba munada komi kasaya mana last month” takalmin kafanta yakalla yace “baki bukatan takalmi” murmushi tayi akunyace tace “eh inaso Baba” ahankali yace “dame kuma” kanta tasauke akasa cikeda ladabi tace “inaso na dinga hijabi sabo wayan nan sun tsufa wasu iron ya konamin, Ya Sa’a kuma ita jakane da takalmi da turare, Farida ma haka, sai Nana ita ribbon takeso da dankunne” jinjina kai yayi yace “shikenan tafi” gyadamai kai tayi cikin cool voice nata tace “Baba Allah ya tsareka yakara daukakaka Allah bada sa’a yakawo rabo Mai albarka” murmushi yayi yace “Ameen diyar Baba kema Allah miki albarka” murmushi tayi sosai tace “Ameen” sannan tabude kofan motan ahankali tafice tawuce ciki, saida Baba yaga shiganta sannan yajuya motan yawuce tareda ciro numbershi yay dialing number Ammi, wayan na gab da katsewa tadauka, strictly yace “yaran nan sun tafi school”? Ahankali tace “Farida ta tafi” “Nanah fa” Baba yay maganan bawasa, bayabo ba fallasa Ammi tace “naga yau Thursday danace ne kawai abari monday sai takoma gabaki daya tunda bataje tun ranan monday ba” shiru yayi kaman bazaice komiba saikuma ahankali yace “banson kina mini ganganci da karatun yarana, sabida kinga ina rigasu fita shine zaki dinga barinsu bazasu makaranta ba, Allah kaimu gobe I will personally take them to school” cikin kunkuni Ammi tace “kanada lokaci ne ai saisa” cikin fushi Baba yace “me kikace” dasauri tace “ni bada kai nai magana ba” dan murmushi yayi, cikeda son su shirya danshi baiso yana fada da matarshi yace “inda dani kike dana juyo motar nan back nadawo gida nabaki hukunci mai kyau” kaman jira Ammi take tace “bani kama mugunta jiya ba” dan murmushi yayi yana shiga cikin police headquarter nasu da aka budemai gate yace “haka akema mata mai tsiwa” dan murmushi kadan Ammi tayi dayaji sautin murmushin hakan yasa yaji hankalinshi ya kwanta sosai ahankali yace “ina sonki sosai Maryam kinsan da haka ko”? Gyadamai kai Ammi tayi kaman yana gabanta jiki asanyaye tace “nasani” ahankali yace “haka kuma inason yaran dakika haifamin aduniyan nan sosai Maryam” murya chan kasa tace “I know” kashe motan Baba yayi yace “dan haka inaso kome kowani decision zan dauka akansu ne supporting me okay, banso muna fada akan yaran nan” ahankali tace “shikenan bazan karaba” murya chan kasa Baba yace “kada ki kara kiran Yasmeen da dakikiya” tasan maganan nan yafi komi tabama Baba rai hakan yasa tace “kuskurene I promise bazan karaba Baban Nanah” murya chan kasa yace “good! Kemin list na abubuwan dakukeso all ki aikamin tawaya, bari naje na zama CP Commissioner Ibrahim Ibrahim mijin Maryam koba hakaba” kwashewa da dariya Ammi tayi ta wayan tace “hakane bari naje na kunna news na kalla” dan dariya yayi yace “to na barki lafiya” ya katse wayan yana murmushi feeling so happy and at ease nothing beats a happy family, his whole entire family is his everything, he literally lives for them now he can go and collect stars nashi cus he know cewa he deserves it, he’s such a dedicated hardworker both in his field and in this house yay maganan yana fitowa daga cikin motanshi.


EXCLUSIVE IS 5k

GGM IS 1k

Kindly pay into 3107021073 Aisha Muhammad first bank

✨KYALKYALIN KAUNA✨


No comments