Kyalkyalin Kauna 3

 EPISODE 3️⃣









Fitowa daga wanka tayi tana tafiya ahankali sabida yanda tagaji dan yau ta taku, Farida tagani adakinsu tana kokarin cire Hijabin islamiyya itakuma Sa’a bata dakin tana dakin Maman su (Yaya) Farida dake kallon Yasmeen din dataga gajiya karara akan fuskanta tace “Anty Miemie mekika kawo mana yau daga bakery dinku Chef”? Wata doguwan riga Yasmeen taciro daga drawer dakin tasaka sannan tajaye igiyan wankan daga jikinta ta shanya akan kofan dakinsu ahankali tace “anjima zan baki gashinan a leda yanzu muyi salla kafin Baba yazo” dasauri Farida tace “ni banayi” Gyadamata kai Yasmeen tayi tadauki hijabi tasaka ta kabbarta salla, saida Baba yafito yasa dukansu matan suje suyi salla sannan yawuce yatafi masallaci shida yara mazan gidan.


Babban gida ne wanda iyayensu suka rasu suka banmusu bayan sun haifesu su uku suka, Baffa wanda shine Babba mijin Yaya kuma, kowa na gidan Yaya ake cema matarshi, dan kasuwa ne Baffa yana saida kayan hatsi akasuwa, Yaya ce kadai matarshi ta haifamai yara biyar guda 4 maza wanda uku sunyi aure suna aiki agaruruwa daban daban Abba kawai yaragemai da Sa’adatu da basuyi aure ba, dukansu na university Sa’a na 200 level shikuma Abba na 300level, sai Baba shi dan sanda ne yaranshi uku duka mata, Yasmeen ce Babba, sai Farida dakuma Nanah, sai kanninshi da ake cema Baba Karami mijin Hajjo yaransu kananu hudu maza biyu sai yan biyu Hassana da Husaina.



Bayan sallan magrib gabaki dayansu mazan suka shigo gida duka yaran zuwa sukayi gaidasu banda Yasmeen da tana sallan magrib ta bingile da bacci danta bala’in gaji, anatse Baba yakalli Farida dake zaune kusada Ammi akan tabarma yace “ina Yasmeen”? Dan ita kadaine bata tsakar gidan, ahankali Farida tace “tayi bacci Baba” bai damu da abincin da aka kawomusu da zasu fara ci ba tashi yayi ahankali yakalli Yayanshi yace “ina zuwa Baffa ku faracin abincin” idan da sabo kowa na gidan yasaba da yanda Baba yake da yaran gidan ma gabaki daya bawai nashi kadaiba gyadamai kai kawai Baffa yayi, direct dakin yaran yawuce wanda shine atsakiya dakinsu wanda yakenan ciki da falo da bayin wanka da dakin Baffa shima ciki da falo da bayin wanka sai akama yara matan dakinsu awajen babban daki guda daya, da sallama chan kasa yadaga labule yashiga dakin, kwance yaga Yasmeen din akasa tai shane shane tana bacci ga hijabin datai salla dashi agefe babu hula akanta sai kitson kanta dakenan all back dayay tsufa amman gashin baki sidik sai uban tsawo tana shakan bacci, ahankali ya tsugunna akanta hannunshi yakai yadaura asaman kan goshinta jin jikinta ba zafi yasa ahankali yakai hannunshi yabugi kafadarta yace “Yasmeen Yasmeen” cikin bacci murya chan ciki tace “uhn Baba” dan shiru yayi yana kallonta saikuma ahankali yatashi gadonsu katon gaske dan su uku ke kwana adakin, wani zubin kuma Nana nazuwa tace ita wajen Anty Yasmeen zata kwana ba wajen Ammi ba sai su zama su hudu, hijabinta dake wajen Baba yadauka ya kakkabe gadon sannan yadawo yaduka yadagata ahankali yace “tashi kihau gado” cikin bacci yadagata tamike tsaye kana ganin yanda take kasan ta bala’in gaji dan har layi layi take kaman zata fadi da taimakonshi yasata akan gadon tana lumshe idanu cike da bacci sannan yakashe wutan dakin dayake kunne yawuce yafito tsakar gida daga Yaya har Hajjo kowa yabishi da kallo anamai harara ciki ciki itadai Ammi ko kallonshi batayiba dan sosai yau yabata mata rai, zama yayi wajen yayinshi yasa hannu suka cigaba da cin tuwon duk wanda zai shigo gidan saisun bashi sha’awa sabida yanda family suke three brothers da iyalansu suna zaune agidan da iyayensu suka bar musu da iyalansu zaman lafiya kuma kansu ahade. 

Saida suka cinye tuwon sannan yakalli Yayan nashi anatse yace “Yaya gobe za’amini karin girma awajen aiki zan koma Commissioner of Police CP” duka gidan hatta Ammi saida takalleshi cikeda farin ciki yaran sukahau cewa “Baba Allah ya sanya alheri” murmushi yamusu yace “Ameen” su Yaya da Hajjo ma sukace “Allah sanya Alheri Allah tayaka riko” anatse yace “Ameen nagode” murmushi Baffa yayi yace “Alhamdulillah Alhamdulillah shi daman duk wanda yarike Allah haka Allah ke daukaka shi, mutane na yawan cewa ai duk Dan sandan da baya karban cin hanci baya kaiwa ko’ina, ko akasuwa idan ana hiran nan nakan cemusu uhm’uh kada suce haka, inada kani da tunda yashiga aikin yan sanda yau kimanin shekaru kusan sha takwas kenan daidai da cin hancin naira biyar baitaba karba ba kuma ahankali ahankali anata karamai girma gashi yau za’a nadaka CP maiyafi haka? Nan gaba saidai muji an maidaka IG gabaki dayama” Baffa yadanyi shiru tareda daukan ruwa ya kurba sannan anatse yace “a kullum ina fadamaka kowani matsayi kasamu arayuwan nan kayi amfani dashi wajen magance matsalolin al’umma gabaki daya, wajen yaki da rashin gaskiya da kafa gaskiya, wajen taiwakama addinin musulunci, wajen tsare hakkin dan adam da saman da zaman lafiya adoron kasa, ta hanyar kawo karshe sata, kidnapping, shaye shaye, fyade, kisan kai da sauransu, Allah ubangiji yabaka sa’a yakuma tayaka ruko sannan kasani wannan position din amana ce, karkaci amanan sabon seat din nan kaji Ibrahim” anatse Baba yace “naji Baffa nagode sosai” dafashi kanninshi mai binshi yayi Baba Karami wanda shine mijin Hajjo yace “Allah yatayaka riko Yaya” murmushi yayi yace “Ameen” tashi Baffa yayi yace “to kumu tashi mutafi masallaci, kukuma matan sai kuyi naku sallan” dan juyawa Baba yayi yakalli Ammi dake kallonshi cikeda farin ciki dauke kai tayi dasauri ganin sun hada ido dan haushin shi takeji wani kalan murmushi yayi yabi su Baffa suka wuce mosque batare dayace mata komiba.


As usual daman gidan ana sallan isha’i kowa ke shigewa daki dan yara anje school angaji, weekends ne dama yaran gidan basu cika bacci da wuri ba dan ranan baaje boko ba,  Ammi na idar da salla tadauki Nanah datai bacci asaman gadonta tafito waje tashigo dakin su Yasmeen tagansu duka sun kwanta dudda ba bacci Sa’a da Farida keyi ba amman Yasmeen tadade da bacci, kwantar da Nana tayi tareda su tana kallon Yasmeen tace “kin gaji ba dole kiyi bacci ba cikin dare kya tashi kiyi ishan kukuma baraku kashe wutan bane” dasauri Sa’a dakejan lullubi tace “Ammi dan Allah kikasha mana” dan hararansu tayi sannan takashe musu tajawo musu kofan tafito tashiga nata dakin, maida kofan falon tayi tarufe sanan tashiga uwar dakinsu, dan matsakaicin bayinsu da wanda kadai ake aciki ta shiga ta watsa ruwa sannan tafito ta shirya cikin kayan bacci ta fesa yan turarukanta ta kwanta.



Wuraren 10 su Baba suka shigo gidan, direct dakin yara yawuce, shikuma Baffa yana kulle gate, ahankali yatura kofansu yashiga wayan hannunshi ya kunna saida ya dudduba su ganin duk sunyi nisa abacci sannan yasake Tofa musu addu’a yafito tareda maida kofan nasu ya kulle sannan yama Baffa sallama duk kowa yashige dakinshi maida kofan dakinsu yayi yarufe sannan yawuce uwardaka, jallabiyan shi yashiga cirewa yana kallon Ammi dako sallaman shi bata amsaba kuma yasan ba bacci take ba, bayi yashiga bakinshi ya wanko tareda dauro alwala wanda wannan haka yake kullum sannan yafito ya kashe wuta taredayin bismillah yahau gadon, ahankali ya matsa kusada Ammi yakai hannunshi yana kokarin juyoda ita cikin wata kalan murya yace “juyo kimin Allah sanya alheri dan ke kadai ce kika rage baki samini albarka ba” kabarda hannunshi tayi cikin fushi da rashin son yin magana dashi tace “stop touching me” dan shiru yayi saikuma chan yace “kiyakuri to” kaman jira take wani kalan juyowa tayi saikuma ta tashi zaune cikeda masifa amman bamai karfi sosai ba gudun kar ajinsu tace “nagaji da hakurin dakeke bani kullum saikagama cimini mutunci agaban uban kowa sabida yara saika biyoni da daddare kana cemin nayakuri yau bazanyi ba kaji Ibrahim bazan yi ba” shiru Baba yayi jin takira sunanshi yau kai tsaye yasan ranta yabaci, cikin wani yanayi na nuna kunci tace “Ibrahim ka manta cewa nine mahaifiyar yaran nan, nine nadaukesu wata tara acikina, nine nai laulayinsu, haka kuma nine nan nikadai nashiga labour room nasha nakudan yaran nan nahaifosu maisa kake treating dina kaman banson yarana kaine kadai ke sonsu why? Inda ba nine na haifesu ba sai ace eh dama banice mahaifiyar su ba but this girls are mine, nine mahaifiyar su, mesa kakemin abinda kakemin akansu eh Baban Nanah”? Shiru Baba yayi baice komiba baki Ammi tabude zatai magana sai kawai kuka ya kufce mata kawai tafashe da kuka sosai dan abinda yake mata na kona matarai ainun, wani kalan sanyi jikin Baba yayi ahankali yajawota zuwa jikinshi batai musu ba tashige bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi yace “kiyakuri bazan karaba, I know you love our girls beside yaranmu ne nidake muka haifesu sometimes ina miki fadane sabida sakaci, Maryam yara mata muka haifa guda uku, hakki ne su akanmu nida ke we have to protect them, support them, musa idanu akan lamarin su, mu tarbiyantan dasu da kyau kinsan idan ka tarbiyantan da yara mata da kyau ka aurar dasu  Allah zai bamu aljanna ranan gobe kiyama? Hadisai daban daban daga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi inda yake nuna falalan da iyaye suke samu ranan gobe kiyama dasuka tarbiyantan da yara mata da kyau, Please understand me kidaina fushi dani, inaso kiyi tsayin daka kaman ni akansu that’s all stop crying matata, I am simply doing the right thing” yay maganan yana bubbuga bayanta, da kyar tai shiru ta dago daga jikinshi sannan takalleshi dudda cikin duhu ne tace “I understand abinda kake kokarin yi kan yaran nan perfectly well but is too much! You are overreacting, Yara mata garemu kana tareda yaran nan 247, kana yawo dasu kana rike musu hannu a anguwa, anguwan nan kap babu wanda baisan how protective you are towards this kids ba, wazai taba zuwa ya aure su kowa tsoron tinkaranka yake, Yasmeen dinmu is 20yrs kasan mates nata guda nawa sukai aure yanzu alayin nan kadai? Ita ko saurayi batadashi sabida kai, kowa yasan babanta dan sanda ne kuma bai bari akula yarshi” Haderai Baba yayi dasauri kaman bashi ba yace “nina gayamiki aurar da ita zanyi yanzu?” Dasauri itama Ammi dan yau kome zai faru yafaru daidai take dashi tace “to karatu kakeson tayi da kana gani dai she is not going anywhere akaratun”? Shiru Baba yayi yajuya kawai zai kwanta dasauri Ammi tarikemai hannun tace “Ibrahim listen to me ba lallai saikabi abinda nake fadi ba amman inaso kai nazari kan maganata, nagaji damaka shiru ne so I have to tell you abinda ke raina yau, Baban Nanah” Ammi tai maganan asanyaye tace “Yasmeeen tun tana yarinya bansan ko dan ita yar fari bace amman dai me and you munsan tun tana yarinya batada kokari, adaddafe a repeating da chanje chanjen makarantu daban daban sabida kai kanka kagaji da repeating da ake mata aka samu tagama sakandare at the age of 18, tai waec na farko duka f9, waec din daka biyamata tana 19yrs Allah ya taimaka taci shima Allah kadai yasan tayaya tai passing dan am sure kai karan kanka har yau u are still in shock ya yanda tai passing exam din, har yau har gobe bakomi Yasmeen ke iya gani takaranta tsaf ba wani zubin Farida nan kanwarta that is just 15yrs SS3 student ke taimakonta dasu Sa’a, dudda babu kalan lesson teachers da lessons dabaka sata ba, Yasmeen is just like that haka Allah yayo brain nata, I am sorry to say this banson nakira yarda na haifa dakikiya amman me and you munsan cewa kusan hakanne, ka kaita school of nursing tafara anayin weeding exam nasu aka koreta batai passing ba shima F tasamu, dudda lokaci yakuri ni nasan dayaya dayaya kasamu da kyar kasamo mata admission na FCE part term shima yanzu tafara an bata Islamic studies amman she’s not going anywhere with it, infact ni aganina ma FCE yafi bata wahala kan school of nursing, subject daya kusan malamai ashirin akai Baban Nanah kuma kowa da nashi abubuwan karatun ina kakeson yarinyar nan tasa kanta?” Ammi tai shiru tana kallon Baba ganin yaki magana yasa ahankali tace “nasan ka hadata dawata lecturer daka biya tana zuwa office nata ana kara maimaita mata komi sannan da kanka kadauketa ka kaita school na Maman Intee nakoyan su abinci, drinks da cakes which shine abu na farko danaga Yasmeen tasoma iyawa sharp sharp tunda na haifo yarinyan nan” Ammi tai shiru sai alokacin Baba yajuyo yakalleta yace “all lissafe lissafen nan what are you trying to say? Nagayamiki nagaji da kashe kudina akanta ne? Koko kintabaji nai korafi kan rashin gane karatun ta dawuri ne? Ai ni ke biya bakeba ko to ki barni da maganan nan please bansonji” girgiza kai Ammi tayi trying to make him understand her tace “Baban Nanah, abinda nake kokarin cewa shine you might thing abinda kakema Yasmeen shine the best thing any father zaima diyarshi but you are wrong yarinyar nan is going through a lot nine mahaifiyarta kwayan idanunta kadai nake gani nasani, karatun nan yamata yawa, sannan yanda ka tsaya tsayin dakan nan akan yaran nan baka basu breathing space karage, let this children be ko masamu wani yayi approaching Yasmeen da maganan aure, Yasmeeen tayi girma, she’s a very fine beautiful girl, give her space wannan kaita FCE dakake duk Saturday da sunday sannan ka koma ka daukota kabari, let her go on her own and mingle da dalibai irinta, allow Yasmeen kullum tadinga zuwa shagon Maman Intee da kanta, stop holding hannun Yasmeen a anguwa kowa nagani yes ansai kai babanta ne but stop treating this children kaman zaka maidasu cikinka u are being over protective and yaran da maza suka gani daddy’s girls ne tsoron approaching nasu ake barinma kai da u happen to be a police man uniform mutum, kar halin nan naka da tsayayyen uba yasa yarana su rasa mijin aure” wani kalan dogon tsaki Baba yaja yace “maganan banza maganan wofi” kawai ya kwanta tareda juyamata baya Ammi tadade tana kallonshi dama deep down tasan za’ai haka shifa indai kan yaranshi ne bayaji bayagani, abinda yayi shine always best akan yaranshi, tadade ahaka sannan takoma ahankali kawai ta kwanta itama tajuyamai baya kowa da abinda yake tunani, almost 20min suna ahaka sai kawai Baba yajuyo dudda yaso yabarta yahakura kasawa yayi cikeda masifa yace “bani hakki na, kuma wannan abun dana barki kikaje aka makala miki a hannu gobe karna dawo aiki naji shi a hannunki, nafasa dagamiki kafan haihuwa nakeso yara uku sunmin kadan” dukfa fitinanta mijinta yafita tanaji tana gani haka yashiga yin yanda yaga dama da ita kaman ma punishment yake bata, duk yanda takai ga jin haushin shi saida tashiga bashi hakuri sannan yasata ajikinshi Ya matse sosai yace “dagayau kada ki kara fadamin wata magana akan yarana, ni mahaifin su ne bazan taba cutar dasu ba, nafiki sanin abinda yadace akan yarana, inason yarana sama da rayuwata, inason yarana sama da zuciyata, my children are my entire life and reason for my existence, inhar kinason mu zauna lafiya ki koyi sonsu kaman yanda nake sonsu dan indai wannan abin dakike fadamin nayi aganinki shine so to kinyi kuskure ba so bane, idan abinda nake musu shine zaisa kada su sami miji to kada su samu din bangaji dasu ba ban gaji da ganinsu ba bazan taba gajiya da yaran da Allah yabani ba, sai maganata ta karshe kada ki kuskura ki kara kiramin yarinya da dakikiya Yasmeen ba dakikiya bace, my daughter is smart, ranan dana fara kaita makaranta aduniya ko A bata iyaba amman yau anwayi gari ta iya A har Z, ta iya 1234, tasan abubuwa da dama, kisan banbancin tsakanin wanda baya iya gane abu dawuri kokuma karanta abu da wuri da dakikiya, kada ki kara kwantata mini yarinya da mummunan kalman nan kinajina” gyadamai kai Ammi tayi dan sosai taga ranshi yabaci sakinta yayi yajuya mata baya yay bacci abinshi yabarta tana matsan hawayen tsantsan bakin ciki.


No comments