Kyalkyalin Kauna 23

 EPISODE 2️⃣3️⃣










Yana bude kofa yafito daga dakinshi wani lafiyayyen kamshi ne yadaki hancinshi da saida ya tsaya yakalli ko’ina dan yasan kamshin abinci yakeji gidan nan ba’a taba daura abinci ba saidai asaya, wani kalan kuka cikinshi yayi dayasa dasauri yakalli cikin shi wlh sai yanzu yama tuna the last time dayaci wani abincin kirki was tun ranan dayaci tuwon nan, dan yatsine fuska yayi yasa bakin eye glasses nashi a idanu na ray-ban dayamai bala’in kyau yafara tafiya anatse cikeda isa, Dan dake zaune a falo tareda su Nas kamshin shi kadai yaji dasauri yamike tsaye yana kallon stairs din, ahankali yake sauka dagakan stairs din wani kalan sanyi yaji na shiga jikinshi at this point yafara yarda he’s sick kokuma zaiyi rashin lafiya ne, dan wannan yawan faduwan gaban, jin sanyi, da tafiya kaman na tsutsa dayakeji a cikinshi is so abnormal, karasa saukowa yayi ya tsaya adaidai gaban last staircase din sosai kamshin abinci ke ratsa hancinshi dayasa cikinshi yashiga lafiyayyen kuka kaman inji abin kaman wani tsafi, gently yajuyar da kanshi ya kalli kofar kitchen dinsu dake wajajen dinning, kaman akwai wani magnet najan kafanshi samin kanshi yayi da fara tafiya yana dumfaran hanyan kitchen din tsayawa yayi agaban kitchen kirjinshi na bugawa hakanan yanajin abubuwa na tafiya acikinshi kafin ahankali yakai hannunshi ya murza handle na kofan yabude, Yasmeen yagani tsaye agaban wani katon pot akan gas hannunta rike da chokalin girki tana juya shinkafan dayan hannunta kuma nakan fuskanta tana share hawayen datake tana kuka, dayan burner kuma wani babban pan ne akai datake soya kajin datai marinating, hannayenshi biyu yazuba cikin aljihun wandon jikinshi yana kallonta cikeda mamaki waya fito da ita wayasata girki, tana cikin juya shinkafan kamshin turaren dataji dazu da safe yawani daki hancinshi dayasa cikin kuka ta hura hancinta tashiga motsi da hancin kaman mai shinshina abu saikuma dawani kalan sauri kaman wacce aka kirata tajuyo takalli kofa hada ido da mutumin dazu tayi dudda yasaka glass sannan yakara chanza kaya from na dazu faduwa sosai gabanta yayi hakanan jitayi takasa jure kallon ahankali tasauke kanta kasa wasu hawayen na zubomata takai bayan hannunta tashare da sauri, strictly babu alamun wasa ko raha akan fuskanshi yace “waya kai dahar yafito dake” kasa dago kanta tayi ballema tamai magana cikin tsawa yace “waya fito dake!” Ba karamin firgita tayi ba dasauri tace “wata mata ce tafito dani” tai maganan tana kara mannewa jikin wajen tama manta wuta ne da tukwane abayanta, bin fuskanta yayi da kallo sai alokacin yaga kululun goshinta hakan yasa yadaga kafa yashigo kitchen din awani kalan firgice tasake matsewa jikin wajen kaman dama abinda gas din keso kenan igiyan hannun riganta yakama dawuta bama ta lura ba, dawani kalan sauri Maheer yace “you hand” kallon hannunta tayi ganin wuta yakama hannun riganta yasa tawani kalan kwara uban ihu da saida yabi ko’ina na gidan su Nas duk suka taso da gudu.


Yana zuwa wurin baiyi wata wata ba wani kalan kama hannu rigan nata yayi bai damu da wutan ba sa hannunshi yayi yakama wutan hakan yasa ta mutu dan kafin yakaita gaban tap zai iya konata sannan yajata zuwa gaban tap yabude tap din dasauri yatara hannunta yana jika hannun rigan da ruwa sannan ya dage hannun rigan cikeda dan damuwa dashi kanshi baimasan yana nunawa ba yakalli smooth brown skin fatan hannunta dake sheki yace “are you hurt? Yakonaki awani waje?” “Ina ruwanka idan ma ta kone”? Kaman daga sama sukaji muryan Hajiya, dawani kalan sauri Yasmeen ta fizge hannunta takoma bayan Maheer dasauri daya dago yakalli Hajiya, arude Yasmeen dake bayanshi tana goge hawaye murya chan kasa ta yanda daga ita sai Maheer zasu iyajin maganan datakeyi tace “please kada kabari ta dakeni, please kaji dan Allah tsoronta nake sosai, she’s wicked” wani bakin lukukin abune ya tsayama Hajiya awuya ganin yanda yarinyar ta makale abayan kaman zata shige jikinshi shikuma Maheer ko matsawa beyiba balle gezau kaman ma abu take gayamai yana saurara, akufule tana kallonsu tace “wlh wlh idan baki fito daga bayanshi kinje kin duba abinda ke wuta ba saina kasheki na rantse da girman Allah” wani kalan mugun kallo Maheer yama Hajiya cikin kakkausan murya yace “wayace ki fito da ita daga inda na kulle ta” cikin tsantsan kishi dayakasa boyuwa a fuskan Hajiya tace “akanme bazata aikatau ba ubanta na chan yana ganama drivers namu azaba”? Strictly Maheer dake kallonta yace “get out!” Kallon kanta Hajiya tayi ga su Nas da Wike duk awajen yana cemata get out zata kara magana yadaka mata wani kalan lafiyayen tsawa da ita kanta Yasmeen saida ta firgita ta duka kasa yace “I said get out of this kitchen!” kallon Maheer Hajiya tayi saikawai tajuya tafita da sauri suma su Nas kaman munafukai juyawa sukayi suka fice daga kitchen din ganin yanda Pablo yama Hajiya ihu kaman yarshi kuma tai biyayya, karasawa gaban gas din yayi yakashe komi sannan ya tsaya awajen yadan kalleta yanda ta tsugunna takasa kallonshi sai goge fuska take da bayan hannu, wani iri yaji saikuma yadauke kai akufule yace “come here” ba musu tazo ganin yanda kowa na gidan ke tsoronshi yake musu ihu daga gani babban azzalumi ne, harta karaso gabanshi tadan tsaya nesa dashi kallonta yake abincin yakalla yace “angama”? Girgixamai kai tayi batare data kalleshi ba, wani iri yaji hakan yasa yadauke kai yace “meya rage?” Ahankali kaman yar yarinya tace “saucing kazan, xan maidashi papered chicken” agogon hannunshi yakalla yace “yi sauri kiyi yunwa nakeji I hope ba rubbish kika dafaba, rubbish mai uban kamshi” yay maganan yana wucewa wajen kujerun dake jere gaban island na kitchen din yazauna yace “make it be fast” gyadamai kai tayi kaman yar baby tasa spoon ta tsamo kajin sannan tashiga hada sauce din bayan ta kunna gas, tunda take aikin ko cire idanu na 1sec baiyi daga kanta ba, he don’t know but kawai dai he don’t know, baimasan dalilin dayasa yake mata kallon nan kaman zai cinyeta da idanu ba, baitabajin yakosa yaci abinci ba sai nata badan komi ba saidan yanda cikinshi ke masifan kuka sabida yanda kamshin girki ke neman hallaka shi.



Cikin 4min tagama tsaf takashe gas tajuyo takalleshi hada idanu sukayi dudda akwai bakin glasses a idanunshi but tasan ita yake kallo, sauke kanta tayi kasa ahankali tace “nagama” dan yatsine fuska yayi kafin ayangance kaman wanda ake roka yace “samin kisama kanki” saida yay maganan yadan kalli bakinshi to meruwanshi datasama kanta ko karta sama kanta, wani plate mai kyau tadauka ta zubamai Chinese fried rice data dafa mai kwai aciki tasa peppered chicken guda 3 akai sanan tadaura a plate, wajen fridge na kitchen din taje cucumber da apple kadai tagani agidan hakan yasa tai cucumber and apple drink a juicer nasu tajuye a jug, jug din gabadaya taciro yay sanyi sosai tadaura akan tray din da cup tasa spoon sannan tadauko tana tafiya ahankali sai kallonta yake takawomai gabanshi ta ijiye batare data kalli fuskanshi ba, koda abincin ba dadi he must give her the credit na plating na abincin is super beautiful, abincin looks appealing ma idanu, daukan tray din yayi yace kisa naki kifito ki sameni a dinning, fitowa daga kitchen din yayi kallo daya yana Hajiya dake zaune a falo sai karkada kafa take kaman wacce ta zare tabishi da kallo cikeda mamaki ganinshi da tray na abinci, dinning yawuce ya ijiye abincin yadago kai yana kallon kofan kitchen jin shiru yasa yamike tsaye gaban kitchen din yayi rakube yaganta agefen kofa rike da plate tazuba shinkafan kadan da nama daya da cokali, fuska daure yace “go and get water” gyadamai kai tayi tajuya tadauko bottle water guda daya, juyawa yayi yace “follow me” fitowa tayi kanta akasa kaman kace ci ta kwasa dagudu corridor yayi wani daki dake kusada study nata yabude sannan yajuyo yakalleta kanta akasa tawuce tashiga ciki daki mai kyau ga lafiyayyen gado, shiga yayi yazare key bayan kofan zai wuce yafita dasauri tace “Hijabina yana wajen su Farida kadauko mini” wani kalan juyowa yayi yakalleta tareda sa hannu yazare bakin glasses na idanunshi ya zubamata idonshi dasauri tasauke kanta akasa, cikin wani shegen murya yace “aikena kike?”.


Zaki iya samin Episode din a IG, makesure kinyi following dina💃💃


Kubu link din nan dan karanta 24 only on IG


https://www.instagram.com/p/CtZbFX-oXma/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==

✨KYALYALIN KAUNA✨




     ✍🏻M SHAKUR



No comments