Kyalkyalin Kauna 20

 EPISODE 2️⃣0️⃣








ZAKI IYA SHIGA GROUP DIN DANAKE POSTING ✨KYALKYALIN KAUNA✨TA HANYAR DANNA LINK DIN NAN



https://chat.whatsapp.com/HyR79BijM7XFBaNPrFcBYn




***

Daga Baba dake wajen aiki harsu Ammi dake gida babu wanda ya runtsa ranan, dan saida dare yayi Ammi ta birkice sosai dan all this while bata yarda anyi kidnapping yaranta ba saida dare yayi, dare yayi taga yaranta duka basa tareda ita an daukesu kenan yanda take kuka sosai saida Baffa yafita yakira wani likitan anguwansu yazo yama Ammi alluran bacci sannan suka samu tai bacci.



Shima Baba dake station baiyi bacci ba saida ya sumar da direba daya cikin direbobin har saida su Aliyu suka fito dashi daga dakin amman direbobin nan sunki magana ganin yanda ya sumar da dayansu kuma yake fushi yasa suka gane Pablo yadauki wani abu nashi that means sun kusa fita hakan yasa suka kara dake ransu sukaki bada any information dan dasuyi betraying organization din dake basu mahaukacin kudin nan dabasu taba samun irinshi arayuwan su ba gwara su mutu a police station din dasu bada information akan Pablo.



Wuraren 7:15 na safe Baba na zaune kan dogon kujeranshi ya lumshe idanu hannunshi rikeda wayan da babu abinda yake sai fatan Allah yasa Pablo yakirashi Aliyu zaune gefenshi daya damu sosai wayan hannun nashi yayi kara hakan yasa dasauri yabude wayan hannunshi har rawa yake saiga video, Yasmeen ce tafara kokarin karatu saida Farida dasuke bayanta itada Nanah sun kankameta tafito takarba tafara karanta abinda ke paper da yanda tafashe da kuka akarshe, yaran sunyi zuru zuru kaman sunyi shekara dari hannun criminals, kasan sau goma Baba yakalli video sannan yakalli Aliyu yabashi wayan yace “sake kiramin number” dialing number Aliyu yayi kaman tsafi number yayi ringing dauka akayi dasauri Baba ya karbi wayan yace “Hello Pablo” Dan ne yayi magana yace “Oga is unavailable, yariga yamaka kiran dazai maka trust me har abada Oga bazai kara kiranka ba kuma” ijiyan zuciya Baba yasauke ahankali yace “hope my children are fine” dasauri Dan yace “absolutely” ahankali Baba yace “zan saki kayanku yanzun nan bada jimawa ba amman shipment din zan fara saki sainaga yarana zan saki direbobi ku” dan murmushi kawai Dan yayi kadan yace “deal namu is direba da kayanmu, nonetheless Oga always keep promise nashi, za’a kai shipment namu trailer park a ijiye we will take it from there” Dan na maganan ya katse wayan Baba yawani kalan fuzar da ijiyan zuciya abin namai kaman bashiba baitaba sanin wani abu zai iya faruwa dazaisa yayi compromising any case ba sai yau! Bude idanunshi yayi ahankali yakalli Aliyu yace “get the boys ku dauki motocin ku kai inda sukace” dasauri Aliyu yace “direbobin fa” lumshe idanu Baba yayi yace “sainaga yarana tukunna” ijiyan zuciya Aliyu yasauke yawuce kawai yafita wato Baba akwai taurin kai shi bazai iya magana ba Ogan shine he must obey abinda yace amman har cikin ranshi yaso Baba yasaki komi nashi,  samin yaranshi yayi dasuka iyajan mota aka kwashi motocin aka tafi dasu har zuwa tipa garage din akai parking tsayawa sukayi suka shige cikin mutane trying to see wanda zaizo yadauka. Baba na zaune a office wayan yayi kara dasauri yadauka cikin kakkausan murya Dan yace “call your boys kace subar wajen nan kafin Oga ya chanza mind dinshi” dip ya katse wayan dasauri Baba yakira Aliyu yace subar wajen dan dole suka tare keke suka shiga sukabar wajen.

***



Fitowanshi daga wanka kenan yana daure da wani short towel a waist nashi da karami a hannunshi yana tsane kanshi, knocking akayi saida yakarasa kan couch dake dakin ya zauna sannan yace “shigo” shigowa Dan yayi cikeda girmamawa yace “Sir munyi securing shipment din komi lafiya lau saidai bai saki direbobin mu ba” dan gejeren murmushi Maheer yasaki sannan yay crossing kafa daya kan daya tareda ijiye karamin towel din a gefenshi sannan yadago kai yakalli Dan yace “kasa Wike to drop the 2 kids, abar babban anan” gyadamai kai Dan yayi yace “yes sir” yajuya yafita daga dakin.


Farida da Nanah nazaune adaki kaman marayu idanunsu sun kumbura kaman babu komi Wike ya shigo da yaranshi dasuka rufe fuskokinsu yana dariya yace “hip hip hurray, time to go home children” fashewa da kuka Nana tayi Wike yamata wani mugun kallo yace “dabakin ta kaman na kifi ke dauketa kafin na bugamata bindiga tasume, mutafi” dasauri Farida dake sanye da hijabin Yasmeen ta dauketa tana leken kofa ganin bataga Yasmeen ba saikuma tai tunani kila tana mota, wani bakin yadi Wike yasamata a fuska yasama Nana sannan aka kama hannunsu aka fita dasu faduwa kawai gaban Farida yake Nanah sai kuka take tanaji aka sasu a mota bata sake sanin ina sukeba sai tafiya suke hankalinta yaki kwanciya, ita batasan iya dadewan dasukai a mota ba but akalla sunkai awa daya sannan taji motan ya tsaya awani waje aka zare hulunan kansu aka bude kofa Wike yamata wani mugun kallo yace “ku sauka”dasauri Farida ta jujjuya takalli motan ganin bataga Yasmeen ba yasa tace “ina Anty Yasmeen”? Wani mahaukacin kallo da Wike yamata yasa tasauka daga motan da gudu tana daukan Nana a hannu yace “idan kinje gida ask your Daddy” sannan sukaja motan dawani kalan bala’in gudu, bin inda suke Farida tayi da kallo sai yanzu tagane ashe agaban school nasu take, goya Nana tayi abaya tashiga tafiya dasauri sauri gudu gudu dan gani take kaman zasu kara zuwa su daukesu kuma tai gida dan basu da nisa sosai da gida, daga Baffa, Baba, da Baba Karami da Aliyu police duk suna tsaye a kofar gida dan yanzun nan Baba yadawo tareda Aliyu baima iya ya shiga cikin gidan ba, kaman daga sama yaji ance. “Babaaaa” dasauri yajuya, hango Farida yayi goye da Nana tana gudu kaman mahaukaciya dawani kalan sauri dagashi harsu Baffa sukayi kanta yana zuwa Farida batai wata wata ba tafada jikinshi sai kuka Baffa kuma ya karbe Nana daga bayanta, dago Faridan yayi daga jikinshi bakinshi har rawa yake yace “i…….ina….ina Yasmeen?”.


✨KYALKYALIN KAUNA✨



     ✍🏻M SHAKUR



No comments