Kyalkyalin Kauna 17

 EPISODE 1️⃣7️⃣







Shop with Tilly gidane na saida kayayyaki daban daban na zuwa office da outing, tops, pallaxos, dogayen riguna da sauransu.

Chat them up don saya now💃💃💃



wa.me/+2348033623392


Tun wajajen 4 da ita da Farida suka tashi kusan atare dakin Farida tabi da kallo sannan takalli Yasmeen, cikin sanyin murya tace “Anty Yasmeen har yanzu muna nan wajen”? Gyadama Farida kai Yasmeen tayi ahankali, dawowa kusada Yasmeen Farida tayi cikin wani kalan siga na hopelessness tasa kanta akirjin Yasmeen tai lamoo ahankali cikin wata kalan raunanniyan murya dake cikeda damuwa sosai tace “Anty Yasmeen tsoro nakeji sosai, ji nake ajikina kaman kashe mu zasuy….” Dawani kalan sauri Yasmeen tadagota tareda kai yatsanta kan lips nata rai abace tace “shush, don’t say that” takai yatsunta dasauri tashare hawayen daya gangaro dagakan idanun Faridan datakoma kaman wacce tai ciwo na shekaru dari tace “babu abinda zan bari yasameku sai inda karfina yakare, i will protect you and Nanah with my life, babu abinda zai sami kannina karkiji tsoro kinji, zamu koma gida I promise you, nasan duk inda Baba yake yana iya yinshi mukoma gida, we are all going home kinji Fariri” Gyadamata kai Farida tayi saikawai tasake shigewa jikin Yasmeen kankameta sosai tayi tana kuka ahankali mara sauti, duk yanda kuka kecinta saitaji ita takasa tahau bubbuga bayan Faridan ahankali ga jikinta yay zafi sosai kanaji kasan zazzabi ya shigeta, sun dade ahaka tacirota daga jikinta tace “zomuje muyi salla” daga Faridan tayi itama ta mike tsaye cikinta nawani kalan murdawa amman ta daure, bayi suka shiga Farida tafara fitsari tayi tsarki itama tayi sannan kowacce tai alwala bayan sun dirje bakinsu da hannu fitowa sukayi, Farida takalleta tace “dame zaki sallan Nanah tai fitsarin kwance a hijabinki damuka lullube dashi” ahankali tashiga warware kullin datama dan kwalinta awuya ta sake maida wani tace “da wannan zanyi ke kiyi da karamin dakikasa” sannan ta kabbarta sallan Farida ma ta kabbarta sukai salla sun dade kowanne addu’a yake Allah ya tsira dasu, pillow Nanah tayi da cinyan Yasmeen atare suka shiga karatun Al Qur’ani ahankali suratul Mulk sai wuraren 6 Nanah tafarka da lafiyayyen kuka kaman ana yankata dasauri daga Yasmeen har Farida sukai kanta hannunta Yasmeen tadaura akanta tana daukanta jikinta zafi itama damuwa sosai Yasmeen tayi tace “Nanah zazzabi kikeyi” cikin kuka da shagwaba irin na yara ta ture Yasmeeen tana sake ballewa dawani kalan mahaukacin ihu tace “Ammiiiiii, Ammmiiiiiii naaa” rasa yanda Yasmeen zatasa kanta yasa ta tsugunna agabanta tareda juyamata baya tace “Oya to hau baboo muje na kaiki wajen Ammi, Farida dauko kayanta abayi nasa mata mutafi” hawa bayan Yasmeen Nana tayi da sauri itakuma Farida tawuce bayi fitowa tayi takalli Yasmeen tace “kayan basu busheba kaman yanzu kika wanke Ma” ihuuu Nana ta tsala tace “ni ahaka zansa wajen Ammi zani” dasauri Farida takoma bayin takawo kayan karba Yasmeen tayi tana sauko da ita daga bayanta ga jikin Nanah zafi rau kaman wuta tace “Nanah kayan nan zasu kara miki zazzabi” fizge wandon kayan makarantan tayi cikeda rigima irin na yara tashiga sawa, tasaka rigan kan singlet na Farida dake jike da fitsari ajikinta itakuma Farida tawuce tadauki hijabi din Yasmeen takai bayi ta dauraye ta shanya aruwa tadawo dakin tana kallon yanda Yasmeen ke jijjiga Nanah dake kuka sosai abayanta tana kiran Ammi ita bama Nanah kebata tausayi ba Yasmeen kebata tausayi ita kadaine bataci komiba cikinsu tun jiya wani kalan mahaukacin bugo kofan dakinsu akayi dayasa dukansu suka firgita dagudu Farida tai tsalle daganan gaban bayi zuwa bayan Yasmeen itakuma Nanah ta dirko daga bayan Yasmeen din taboye abayanta itama kaman Farida tana rusa uban kuka, hakanan Yasmeen taji kirjinta nawani kalan extraordinary bugawa takalli kofan lips nata har rawa suke takai hannayenta tana kara kankame su Farida dasuka boye abayanta, bude kofan akayi wasu maza biyu da fuskansu ke arufe ga bindigogi ahannunsu suka shigo dawani lafiyayyen royal chair kaman irin kujeran sarkin nan suka ijiye kujeran nesa kadan dasu Yasmeen but kujeran na facing nasu, dayan yace “gyara zaman kujeran kada mubata ma Oga rai this early morning” gyara zaman kujeran sukayi suka juya suka fita dasauri batare dasun kalli su Yasmeen ba, sake kankame kanne ta Yasmeen tayi tana karanto duk wani addu’a data iya sabida yanda gabanta kewani kalan mahaukacin fadi daidai lokacin aka kara bude kofan wasu kattin maza wanda jikinsu kadai tagani tagane security ne su dudda fuskokinsu arufe but suna sanye da suit suma ga bindigogi a hannunsu sunyi charko charko sun kame jikin kofan daidai lokacin wani kafa dake sanye cikin black wando dayasha guga da black covershoe na Gucci dake kyalli yashigo dakin, dawani kalan sauri Yasmeen ta lumshe idanunta sabida wani kalan arnen sanyi dataji tanaji dahar saida hakoranta suka hade sukai kara kaman vibration grrrr!.


Kaman wani sarki yawani kalan tako yana tafiya dai dai yataho ya zauna akan kujeran da aka ijiyemai yay crossing kafa daya akan daya idanunshi sanye cikin wani baki kirin glass na police dabaka iya ganin idanunshi jikinshi danye da suit dayamai bala’in kyau yazauna ajikinshi kaman dan shi akai suit aduniya, tsayawa Wike, Nas da Dan duk sukayi abayan kujeran dayake zaune duka fuskokinsu arufe banda Wike duk suna kallonsu Yasmeen banda shi dahar yanzu bai daga idanunshi yadaura akansu saima zuba hannuwanshi dayayi saman hannun kujeran yay crossing legs nashi ta hanyar daura kafa daya akan daya.



Wani kalan kamshi da tunda take arayuwanta bata tabajin kamshi mai kwatankwacin dadin nan bane yadaki hancinta dayasa tadaure tabude idanunta ahankali dan kadan takalli gabanta daidai shima yana dago kanshi dan kallon yaran for the first time suka hada idanu dudda idanunshi na cikin bakin glasses. Wani kalan faduwa gaban Yasmeen yayi dasauri tasauke kanta tareda sake maida idanun ta lumshe kallo daya tamai tagane shine Ogan sabida kalan zaman kadai dayayi akan kujeran, dauke kanshi yayi tareda dan girgiza kanshi kadan sabida yanda Nanah ke kuka yana shiga kanshi, he hates children and he hates kukansu, daurewa yayi ahankali yadaga hannunshi sama hakan yasa dasauri Dan yaciro kwalin cigar dinshi yaciro daya yasamai a hannu sannan yazo tagaban shi ya kunna lighter akan taban hakan yasa ahankali Maheer yakai taban bakinshi ya zuka kadan tareda dan runtse idanu jijiyoyin kanshi har mimmikewa suke sabida yanda kukan Nanah ke damun kwakwalwan shi, sake kai taban bakinshi yayi zai zuka kawai yakasa controlling kanshi yayi mugun loosing cool nashi cikin wani mahaukacin tsawa da saida dakin yawani amsa yace “Ke!” Ba Nana ba har Yasmeen da Farida dukansu saida suka firgita, cikeda bacin rai dakuma daka tsawa kaman dakin zai fashe yace “shut up!” Wani kalan zabura Nanah tayi tana kuka sosai kaman zata mutu ta kankame idanunta tana kwakume Yasmeen gamgam ta bayanta kaman zata barka mata riga irin yanda yara keyi din nan idan sunga wanda suke tsoro tace “Anty Yasmeen Ammi Ammiii” tana maganan tana makyarkyata tana sakin fitsari bin fitsarin fitsarin Maheer yayi da kallo datakeyi tana kuka cikin fushi yakalli Wike yace “why did you bring this child to my house bayan kasan how much I hate children haaaa, shoot her idan batai shiru ba!” Dawani kalan sauri Yasmeen tadago kanta takalleshi tana boye Nanah abayanta da kyau gabanta na bugawa ita bama tasan ko kallonta yake koba kallonta yakeba sabida glasses na idanunshi but dai fuskanshi na kan kallonsu ne, cikin wata kalan muryan dake cike da tsoro mai kuma mugun sanyi tace “she’s just a child that is very scared, idan da wacce zakasa a harba adakin nan should be me! Not my sisters” for the first time Maheer zubama Yasmeen manyan idanunshi yayi dudda ta cikin glass ne kasa jurewa tayi tadauke kai da sauri ta tsugunna tareda kallon Nana da idanunta ke kulle gamgam kaman na Farida ahankali tashafa kanta da fuskanta tace “kiyi shiru Nanah kinga Uncle bayason kukan yara, please Nanah zan kaiki wajen Ammi idan mungama kinji yi shiru to Nana na” gyadama Yasmeen kai tayi ahankali ta rungume Yasmeen da sauri, ahankali Yasmeen ta mike tsaye tareda sauke Nanah taboyeta abayanta sannan tasauke kanta akasa tana wasa da yatsunta kirjinta bugawa kawai yake kaman tashin aradu, da hannu Maheer yama Dan alamu yabasu wani takarda da Dan ke rikeda shi hakan yasa Dan yataho gabansu baya Yasmeen tayi dasauri a tsorace ganin wani ya nufota, Maheer duk yana zaune inda yake yana kallonsu, tsayawa daidai gabansu Dan yayi yana kallon fuskan Yasmeen din ganin kaman yataba ganinta amman yakasa tunawa yabata paper tana wani kalan nishi kaman zata shide ta amsa tana kallon paper, Dan yace “wannan sakone zuwa ga Baban ki da zaki karanta yanzun nan zan muku video idan zaki fara karantawa dazamu aika mishi, let’s hope he listens yasaki kayanmu muma musake ku” yay maganan yana komawa baya itakuma Yasmeen na kallon rubutun takardan da takasa gane komi ciki ko abin yahadu da she’s under stress da tsoro ne oho but word na farko kadai ma takasa karantawa ballantana sauran, waya Dan yaciro yakunna video yakalli Yasmeen din yace “kifara nafara video” gyadamai kai tayi ahankali takalli paper tana ware manya manyan idanunta dasuka kara haske tass sabida safiya ne  kwaiduwan idanun sunyi gray sosai tana kokarin karanta word na farkon ma takasa, ahankali Maheer dake shan taba yadago kanshi yadaura mayun idanunshi akan fuskanta yana kallonta tundaga kan hannayenta data rike paper gamgam yatsunta na motsi sosai da dan tiny little red lallen daya rage a kumbunanta, zare hannunta daya tayi daga rikon datama paper takai yatsanta dasauri tadaura akan letters din kaman mai koyan ABCD tace “P……..Paaaaa……” tasake kakarewa dakin yay tsit ana kallonta, kafin takara daddagewa da duka karfinta hawaye na taruwa a idanunta tsabagen yanda take fama ta karanta tace “Paaaa……bu…bu….no….boooo…..” Daidai nan hawaye ya sauko daga idanunta dasauri takai bayan hannunta ta share kwallan tana kara ware manyan idanunta trying to read it by fire by force kowa na kallonta na dakin, ahankali Farida dake bayanta tafito gently tasa hannunta akan paper tareda kallon Yasmeen murya chan kasa tace “kawo na karanta Anty Yasmeen” gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali gwanin ban tausayi sannan tasakin mata paper karba Farida tayi tadan dagokai takallesu kasa kasa dan takasa kallon fuskan kowa kafin tasauke kanta dasauri cikeda tsoro tace “my sister nada matsalan hada baki so I will read” sosai Maheer ke kallon Yasmeen data tsaya gefen Farida innocently har lokacin kwayan idanunta na kyallin hawaye sabida hawaye dasuke ciki, anatse Farida tafara karanta takardan.


“Pablo Escobar yabaka 1hour kasaki his shipment da drivers nashi yasaki maka yaranka inba hakaba zaka tsinci gawawwakin yaranka ukun nan dakake gani akan video agaban police station dinku”.

Fashewa da kuka sosai Farida tayi cikin wani kalan muryan tsoro da tsantsan tashin hankali ganin sunce zasu kashesu tace “Baba dan Allah ka basu abunsu we are scared Baba” katse video Dan yayi yajuyo yakalli Maheer dake kallon Yasmeen har lokacin cikin glass nashi yace “it’s done Sir” gently Maheer yamike tsaye ganin zai juya yasa cikeda Yasmeen tace “kaine Ogansu ko”? Chak Maheer ya tsaya batare daya juyoba hakama yaranshi, Dan yakalli Yasmeen datai magana yace “ke are you okay kike tambayan sir ko shine Ogan mu” wani kalan kallo tama Dan adake cikeda damuwa dakuma jarumta tace “da Oganka nake magana bada kaiba” wani kalan juyowa Maheer yayi kaman zaki jin yanda yarinyar tai magana da saida Yasmeen din tai baya da sauri sannan ta tsaya takalli hayakin taban daya huro tasa hannu ta kakkabe kafin takalleshi tace “inaso kasaki kannena su koma gida ni ku barni anan har lokacin da Baba zai saki kayanku da direbobin ku dakuke so yasaki” sosai Maheer yake kallonta yanda takemai maganan kaman tana bashi command, ganin yanda yake kallonta yasa Dan yabude baki zaiyi magana yadagamai hannu alamun kar yayi, yadda karan taban hannunshi yayi akasa cikin wani kalan husky voice yace “are you commanding me”? Cikin yanayi na matukar bacin rai ganin yanda Ogansu keda rainin wayo yasa tace “I don’t know! All I know is kannina basuda lafiya, kabarsu sutafi niku rikeni bakada imani ne dazakai kidnapping 4yrs old little girl”? Hannun Yasmeen Farida takama cikin tsoro fizge hannunta Yasmeen tayi cikin zafin rai tai ihu tace “ki barni, yadauka tsoronshi akeji ne the worse zai iya shine ya harbeni namutu ko yadade baiyiba, baka da Imani ne”? Sosai abin yabashi mamaki tunda yake babu wacce ta taba kallonshi tamai magana kwatankwacin haka ballema rashin kunya irin na yarinyar nan, wani makirin murmushi yayi tareda shafa sajenshi yana kallonta still kafin cikin wani dan iskan takadirin murya yace “bani dashi ko kadan” yajuya mata baya tareda kallon Dan yace “take this lousy girl and lock her up a study” Maheer yay maganan azafafe tareda juyowa yana kallon fuskan Yasmeen din, zaro idanu tayi tana komawa baya tana kallon sauran mazan dakin dake dumfarowa inda take, Farida tafashe da kuka suna kankame ta, ganin da gaske suke dauketa zasuyi yasa dasauri Yasmeen tace “kayakuri dan Allah karka sa akaini wani waje daban da kannena please please please dan Allah” juyawa Maheer yayi fuuuu yafice daga dakin, Dan da Nas suka bishi abaya, su Farida suna ji suna gani daukanta akayi aka fita da ita daga dakin suna kuka sosai suna kururuwa itama Yasmeen na kuka sosai tana kururuwa aka kallesu  itakuma aka wuce da ita wani waje.


✨KYALKYALIN KAUNA✨




✍🏻M SHAKUR


No comments