Kyalkyalin Kauna 14

 EPISODE 1️⃣4️⃣










Saida yay sallan juma’a wanda shidai yasan yay salla ne amman baida natsuwa sanan yashiga mota yatuko kanshi zuwa gida, duk wanda zai kalli Baba yasan ba lafiya ba, yayi dialing number da Pablo yakirashi dashi yau da safe yafi sau dari but number bayama connecting kaman babu number a network, parking yayi a kofar gida yadade zaune a motan sannan yabude mota yafito yashiga cikin gida ahankali, Ammi yagani zaune atsakar gida idanunta sun jajir kaman kuka tagamayi gasu Kaka da Hajjo akanta da duka yaran gidan harda Sa’a kowa yay zuru zuru, ana ganin Baba Hajjo tace “yauwa ga Baban Nanan nan yadawo” dasauri Ammi ta mike tsaye jin ance ga Baba kafin ma yakarasa idasowa wajensu tayi wajenshi dasauri tace “ina suke, su Hassana kowa yadawo daga makaranta banda Farida da Nanah, naje makarantan principal tace ka aiko a daukesu amman kuma wai kasake kiranta kaman dawani matsala, and yanzu danaga fuskanka nasan da matsalan dagaske ina suke, ina Farida da Nanah?” Kallon fuskan Ammi yayi wato uwa uwace she is feeling something, jikinta yabata ba lafiya, daidai nan aka bude gate, Baffa ne dakuma Baba Karami suka shigo dan dama duk Friday bayan masallaci suna dawowa gida aci abinci kafin akara fita, ganin Baba yasa yace “Ibrahim meke faruwa Maman Sa’a takirani wai ba’aga su Farida ba” yay maganan yana karasowa gaban Baba, fuskan Baba kadai yagani yagane da wani abu babba ma ba karami ba, ganin Baba yayi shiru har lokacin yaki magana yasa Ammi dake kallon fuskan Baba all this while takai hannayenta tadaura saman kanta saikawai tafashe da kuka sosai tace “Baban Nanah ina yarana? Kayakuri ka taimaka kafadamini inda yarana suke zanje dakaina in dauko su, jikina nafadamini they’re in trouble, tunda natashi yau I’ve been feeling somehow ina yarana eh, kafadamini ina yaran……” “an kwashesu!”  Baba yay maganan da ihu ranshi abace cikin wani kalan zafin zuciya, kowa na gidan tsayawa yayi kikam yana kallonshi babu wanda ya iya yay magana, Ammi daura duka hannayen ta tayi saman kirjinta dake wani kalan mahaukacin bugu, Baffa ne yay namijin kokarin iya magana yace “ban gane an kwashesu ba Ibrahima” dan lumshe idanu Baba yayi dan yakasa jure kallon da Ammi kemai kaman wacce ta zare, kafin ahankali yabude su cikin wata kalan raunanniyan murya yakalli Yayan shi yace “Yaya akwai wani case danakeyi da wannan dan kwayan Pablo Escobar….!” Ganin kalan kallon da Ammi kemai yasa yakalli Baffa yace “Yaya na kwace motan kayanshi dasuka shigo na kwayoyi guda biyar da direbobin shi nakama shine yay kidnapping, Nanah, Farida dakuma Yasme…….” luuuuuu kawai Ammi ta tafi a asume dayasa su Hajjo tareta, azafaffe Baba ya karbeta daga hannunsu yana kiran sunanta, Baffa yace “kwantar da ita akan tabarma kawo ruwa Sa’a” da gudu Sa’a tawuce randa tadebo ruwa takawo, yayyafamata Baba yayi a fuska wani kalan ijiyan zuciya Ammi ta sauke sanan ta bude idanu tabi kowa na wajen da kallo kafin ta sauke idanunta kan Baba, dawani kalan sauri ta yunkuro tana kama hannunshi kaman wacce ta zare tace “wasa kake ko Baban Nanah, babu wanda yasace mini yara, Yasmeen na makaranta yau tanada test na Islamic Education wlh, kirata kaji tana makaranta, Yasmeen na makaranta wlh Baffa ni nasani” cikin wani kalan yanayi Baba ya lumshe idanu ganin Ammi na having panic attack surutai kawai take, cikin sambatu Ammi tace “Nanah autana yau batason taje school nasata taje, my little girl yaushe ta warke daga measles, ta gayamini idan tadawo shayi zata sha da buredi I promise, I promise her zan mata, ni nasan tana makaranta babu wanda zai sacemini yarinya she’s just 4, Faridah Sa’a ai Farida batai breakfast yau ta tafi school bako” Gyadamata kai Sa’a tayi idanunta nacika da kwalla sosai, Ammi tace “nasan she’s hungry yanzu bari natashi naje na musu girki dasauri wani abu ne yarike dukansu a school yanzun nan zasu dawo zaku gani, zakugani” arude Ammi ta yunkura tai hanyar kitchen Hajjo tabita da sauri, Baffa ya kalli Baba dayabi Ammi da kallo idanunta sunyi jazur yace “tell me everything” anatse Baba yaciro wayanshi ya kunna hoton ya nunamusu, salati Yaya tayi Sa’a kuma tafashe da kuka sosai koba komi tanason yan uwanta sosai wlh, adake Baffa yace “Ibrahim I know you but akanme zakai case da babban criminal haka idan yama yaran nan wani abu fa? Duk wanda zaiyi kidnapping har yarinya yar shekara hudu ai kasan baida imani yanzu ka kirashi”? Cikeda damuwa Baba yace “number daya kirani dashi batakan network, sai yagadama yakirani shine zan iya magana dashi” cikeda masifa Baffa yace “to meyakeso” ahankali Baba yace “direbobin shi da kayanshi inba hakaba bazai sakesu ba” cikin tsananin fushi Baffa yace “I don’t care about your work, mutumin nan harkan kwayoyi yake bawai dan boko haram bane, kasaki abubuwan shi yaran nan sudawo gida Ibrahim inba hakaba zan yi fushin daban tabayi dakai ba” lumshe idanu Baba yayi cikeda damuwa kaman zai saki kuka, cikeda damuwa sosai yace “Baffa bazan iya sakinsu without proof of life ba, I need to be sure yarana are fine kafin nasaki kayansu” cikeda damuwa Baffa yace “stay with phone zai kiraka, katashi ka koma wajen aiki duk yanda zakayi kayi yaran nan sufito sannan kafita harkan duk wanda ke kokarin illata maka iyali Ibrahim, kaje zan zauna agida mukula da Maman Nanah, if akwai wani abu I will call u just go and handle this issue” tashi Baba yayi kaman wanda kayan cikinshi suka mutu, Yaya tace “Allah ubangiji yafishe yaran nan, Yasmeen da Farida dasuke yammata Ya ubangijin sammai da kassai ka tsaresu ka kare mutuncin su na yara mata ya Allahu, wayyo Allah na mun shiga uku mun lalace wannan wace kalan kaddara ce, yo wayan nan yan fashin ne ko kidnappers kuka kirasu idan sukama yaran nan wani abu fa, yammata Farida sha shida, Yasmeen ashirin na shiga uku na, nan nan faram faram Yasmeen tazo tamin sallama da safen nan har ina bata naira hamsin, Ya Allah ka tsaremini Yasmeen da Farida da Nanah ka karemini mutuncin su”  Yaya tafashe da kuka sosai  tace “ga Maman Nanah chan kaman zarewa ma tayi yo ba dole ba, yaranta kakap uku wasu chan kattan maza su dauke sabida aikin ubansu” juyawa Baba yayi yafice yashiga mota ya kifa kai yana tunani kafin chan yadago kanshi yatada motan yabar unguwa babu abinda ke ranshi irin yaranshi.

✨KK✨



✍🏻M SHAKUR


No comments