Kyalkyalin Kauna 13

 


EPISODE 1️⃣3️⃣








KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;

wa.me/+2347012181461



Office din IG suka wuce wannan karan baima jira secretary yabashi izinin shiga ba Baba ko kallonshi baiyiba yatura kofan kawai yabude yashiga cikin office din, IG natare da mutane but ayanda yaga fuskan Baba yasa yasallamesu yakalli Baba yace “CP lafiya kuwa? Why are you looking somehow”? Karasowa Baba yayi gabanshi ahankali yamikama IG wayan cikin wani kalan yanayi yace “y’ay’ana Oga” dasauri IG yaduba hoton yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un, ya kwashe maka yara”? Dasauri Aliyu yataho leka hoton yayi sanan yakalli Baba, anatse IG yakalli Aliyu yace “daukomai ruwa daga fridge dina yasha” dasauri Aliyu yay wajen fridge dake office din yabude goran ruwa yadauka karami mai sanyi yakawo ma Baba tareda bude marfin, karba Baba yayi saida ya tada ruwan duka sannan ya ijiye goran, anatse IG yace “calm down” gyadamai kai kawai Baba yayi yay shiru shi kadai yasan yanda yakeji, IG yakalli Aliyu yace “yanzu a ina kuke any progress”? Anatse Aliyu yace “babu so far so good su karan kansu basusan waye Pablo ba i believe them, ire iren mutanen nan dama kananun workers irin direbobi haka basu sansu ba, sannan basu bamu address na inda zasukai kwayoyin nan ba, shikuma Pablo yaba CP dama awa daya dazu dasukai waya kan yasaki kayanshi da yaranshi inba hakaba zai aiko mai sako, I guess wannan ne sakon” ijiyan zuciya IG yasauke yakalli Baba dayay shiru kawai yana kallonsu yace “Ibrahim” ahankali Baba yadago kai yakalleshi, IG yace “kai kasan I have only kyaykyawan niyya akanka, nasan cewa daka kawomini case din nan nina baka go ahead akan eh go for it, banyi kuma bantaba tunanin cewa shi wannan Pablo Escobar din kwararren criminal bane dazai iya kidnapping family naka ba sai yanzu, kalleni da kyau Ibrahim” Baba yakalli IG, yace “yaranka are involve in this whole thing now, yaranka ma bawai anyhow yara ba ana maganan yara mata anan kuma kanana karaman chan ma banjin takai 5yrs ba dan haka inaso kasaki kayan nan da dirobobin nan yasakin maka yaranka kafin wani abu yazo yasamesu, tunda yanzu munsan waye Pablo Escobar din, munsan how he operate, munsan how notorious yake zamu shirya mishi da kyau kafin muce zamu kamashi ko jam’iyyan shi muyi case dasu” tunda yafara maganan Baba ke kallonshi baice tak ba, IG yace “your children are mine, I can’t imagine wani kasurgumin dan ta’adda ya sacemini kananun yarana yammata ko aure basuyi ba kasan risk na hakan kuwa Ibrahim? Kasan me this abun nan will do to their future idan duniya tasan Pablo Escobar ya kwashe maka yara, babu wanda zaiso yahada zuri’a da matan da Pablo Escobar yay kidnapping. No no no banmaso nayi wannan tunanin nan Allah ya tsare, dama this whole operation is black operation mu kadai ne muka san dashi muka san abinmu, ko mun sakesu babu abinda zai faru ko wani abu yafaru ma you have me, da sanina akayi komi I can stand for you, kayanshi da direbobin shi yakeso kabashi ka karbi yaranka, family before everything kada kasaka rayukan the only yaran da Allah yabaka aduniya in danger in the name of kanason ka kama Pablo Escobar kanajina Ibrahim, idan baka kamashi ba an kama criminals dubu kuma duka duk kauda mugun daga doron kasa ne” kusan minti daya Baba yayi yana kallon IG kafin ahankali yasauke ijiyan zuciya cikeda damuwa yace “naji yallabai amman ina neman alfarma wajenka” gyadamai kai IG yayi yace “ina jinka” shiru Baba yayi kaman mai tsoron abinda zai fadi kafin cikeda dakewan zuciya yace “dan Allah Yallabai kabarni nan handling this issue in my own way Dan Allah Yallabai kada kabada umurnin asaki kayan nan ko direbobin nan dakanka kabarni nayi decision din idan nagama tunani” baki IG yabude yana kallon Baba kawai, sai chan yace “shikenan Ibrahim daman shawara ce nabaka duk yanda kai handling case din is fine but remember family comes first karkace ban fadamaka ba” gyadamai kai Baba yayi sannan ahankali Baba yatashi yawuce yafita Aliyu yabishi abaya IG ya girgiza kai kawai Ibrahim nada taurin kai na gidi komadai menene Allah ubangiji ya karemai yaranshi.




Office Baba yakoma ya zauna ganin Ammi taki daina kira yasa ya kashe wayan gabaki daya, yakalli Aliyu yace “hoto kawai yatura mini baice wani abu game da hoton ba, na gwada kiran number da yakirani da ita dazu kaman number bata kan network” ahankali Aliyu yace “Yallabai can I say something?” Batare da Baba yakalli fuskanshi ba yace “you can” ijiyan zuciya yasauke, ahankali yace “abinda IG yafada gaskiya ne, yallabai koda ace yau bomabomai yake sakawa akasan nan bama kayan shaye shaye ba, gaskiya da kamashi gwara ka hakura ka bashi kayanshi yasaki yaran nan” cikeda masifa Baba yace “did you look at me kaman mai tsoron wani lowlife stupid drug kingpin eh? Bakasan dama wannan tsoron da shakkanshi shine dalilin dayasa ya kwashe su Yasmeen ba sabida na tsorata nasaki kayanshi da gudu, he can’t do anything to them jikina yabani hakan, he’s a druglord not girl trafficker, babu abinda zai sami yarana I am sure, yes yes” yanda Baba ke magana kaman ya zare hakan yasa Aliyu bai kara fadin komiba, tashi Baba yayi yakwashe duka wayoyin incase Pablo yakira sannan yadauki key motanshi yace “zanje masallaci daganan zanje gida” yawuce fuuu yafita.


KINASON MAGANA DA NI M SHAKUR??? Click on this link and chat me up directly;

wa.me/+2347012181461



✨KYALKYALIN KAUNA✨



    ✍🏻M SHAKUR



No comments