Kyalkyalin Kauna 12

 


EPISODE 1️⃣2️⃣







Maryam Eygpt abaya gidane na abayoyi daban daban na Egypt da sauransu, tana bada sari tana saida daidai abayanta are damn affordable, click on this link and join her group.

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj






Yana zaune kishingide acikin office dinshi ya lumshe idanu kaman wanda ke bacci akai knocking, batare daya bude idanunshi ba hannunshi ya mika ya danna wata botur hakan yasa aka bude kofan office din aka shigo, anatse Dan ya maida kofan yarufe yajuyo yataho zuwa gaban table din, cikeda girmamawa yace “Sir Wike yakawo girls din” shiru yayi still idanunshi a lumshe batare dayay motsi ba, kusan 2min yayi ahaka sannan yabude idanunshi ahankali sundanyi ja kadan ya zubasu akan Dan, sauke kanshi Dan yayi kasa, ahankali yace “kayi abinda nace kama dakin?” Gyadamai kai Dan yayi yace “yes sir”  tashi yayi ahankali dagakan kujeran yadauki kwalin tabanshi dake kan table yazaro daya yasa abaki yadauki lighter ya kunna sannan yafara tafiya kadan kadan yana busan taban yatafi zuwa wajen babban window dake dakin dakenan da wasu hadaddun plain design milk curtains, wani dan remote dake gefen labulen dake makale a bango yakai hannu yataba hakan yasa window yabude, garden ne lafiyayye abayan window da flowers but daga window kana iya hango wani separate building again wanda yakenan ta bayan gidan, ga yaran Wike tsaye gaban flat din rike da bindigogi suna gadi, taban yakai bakinshi ya zuka ya busar idanunshi kyar akan building din kaman mai tunanin wani abu, hannunshi daya yakai yatura a aljihun wando dayan hannun kuma rikeda karan taba yana zuka yana kallon building din chan yace “take that phone kamini snapping nasu all 3 together” dasauri Dan yace “sir the girls are unconscious” batare daya juyoba yace “that’s how I want the pics” dasauri Dan yace “yes sir” yawuce gaban table din wannan special phone din daya kira Baba dashi yadauka yawuce yafita daga office din, Maheer na tsaye yana shan taban yana kallon Dan yawuce yaje building din yashiga ciki ko 1min baiyiba acikin dakin ba yafito duk Maheer na kallonshi ta window yadawo, kai tsaye wannan karan yashigo office din har inda Maheer yake tsaye gaban window yazo yamikamai wayan yace “gashinan nayi hotunan” ko juyowa baiyiba balle yayi alamun karban wayan saida yakarashe shanye taban tass sannan yamikamai hannu batare daya juyoba, samai wayan yayi a hannu hakan yasa yadawo da wayan gabanshi ya danna screen din tai haske saiga Yasmeen, Farida dakuma Nanah, dukansu zazzaune akan wasu kujeru irin na kulle mutanen nan, kujerun nada belt tawajen hannu da wajen kafafu duk an kulle hannuwansu da kafaffuwansu da belt, dukansu idanunsu lumshe suna bacci kansu ya lankwashe babu wacce tamasan inda kanta yake, kusan 1min yabata yana kallon hoton sannan yasa fingers dinshi yashiga scrolling yana kallon 5 different pics da Dan ya dauka nasu checking and rechecking dan tabbatar babu wani abu dazai incriminating ko sanar da komi game da inda suke, sannan yajuya ahankali yakoma kan kujeranshi hoto daya ya zaba cikin hotunan yay sending nashi as MMS ma CP tareda kashe wayan dip sannan ya ijiye agogon hannunshi ya kalla yace “today is Friday yeah”? Dasauri Dan yace “yes Sir” tashi yayi yadauki wayanshi kadai dagakan table din yawuce batare daya jira Dan yabudemai kofa ba yabude da kanshi yafice yawuce sama dakinshi yashiga lafiyayyen wanka yayi yafito ya goge jikinshi yawuce closet yana tsane kanshi wani Riga da wando yadauko na jean dark blue da farin riga yadawo ya shirya tsaf bayan yagama wankan turare, dadduma yadauka ya shimfida sai alokacin yay sallan asubahi sannan yatashi yafito Dan na falo ganinshi yasa yay wajen kofa budemai yayi yana zuwa yafice yace “take me to mosque”.




Wuraren 12:30 Baba na cikin wani kurkuku da ake dukan criminals idan anaso su bada information yana kallon yanda akecin uban direban kan sunada information akan Pablo Escobar amman sai cewa suke su basu sanshi ba basuma taba ganinshi ba iya kansu dauko kaya daga lagos zuwa nan shikenan, address na border ma sunki badawa har lokacin dan kowannensu naji no matter what zasu fito, Baba dake tsaye daga ta waje yana kallon abinda ke faruwa aciki wayanshi ne na office yay karan shigowan sako, dasauri yakai hannunshi aljihun wandonshi yaciro wayan, messege yagani from no number, kawai just sako, hakanan yaji kirjinshi kawai ya buga shi kanshi baisan dalili ba, ahankali yabude message din idanunshi suka sauka kan Yasmeen, Farida da Nanah dukansu basa hayyacinsu an daddaure musu hannu da kafafu, wani kalan wawan bugawa zuciyanshi yayi baisan lokacin da wayan tafadi daga hannunshi zuwa kasa ba, hakan yasa dasauri yakira sunan Allah. “La’ilaha illallah” still kirjin nashi na dukan uku uku amman yadaure yaduka ahankali yadauki wayan yakara kallo gashi nan yaranshi ne tabbas dudda duk suna bacci basa hayyacinsu, ga Nanah da Uniform, Farida ma sanye da uniform na school nasu, dasauri yajuya yafita daga dakin yaciro dayan wayanshi yashiga dialing number Ammi yana tafiya da sauri da sauri kaman mahaukaci, ringing daya biyu Ammi ta daga kafin tama gamamai sallama yace “Nanah taje school yau ne”? Ammi fushi takedashi sosai but jin yanayin muryanshi yasa tace “eh taje meya faru”? Shiru yayi yakasa magana saikuma ya katse wayan da sauri tunawa da yanada number principal din school nasu dasauri yanemo number ta yayi dialing, wayan na gab da katsewa tadauka tace “yallabai congratulations naga karin girman da aka maka, nasan hala kana kirane dan kaji ko su dawo an gama musu interview ko, Farida zata iya dawowa ita sai 3:30 dama, Nana ko kawai kawuce da ita gida” Baba ji yayi magana na neman gagaranshi ga Ammi sai kira take yana shigowa as call waiting, da kyar Baba ya tattaro natsuwa shi yace “ban gane abinda kike fadi ba, ina sukaje Farida da Nanah?” Baki principal tasaki tace “a’a, dazun nan ba ka aiko wani dan sandaba yasa Uniform sunanshi Aliyu SS nagani a tag nashi wai kace yazo ya kawo maka Farida da Nanah station za‘amusu interview, namaso nakira ka yace kana meeting” Baba ji yayi kaman iska na dibanshi Aliyu natare dashi a station tun jiya har yanzu, yanzu da gaske an dauke yaranshi, katse wayan yayi dasauri daidai wayan Ammi nasake shigowa hakan yasa yadauka yakai wayan kunnenshi yay shiru yakasa magana, anatse Mama tace “Baban Nanah meke faruwa wai? My mind is telling me something, tun safe yau natashi gabana sai faduwa yake yanzu kuma yadadu meke faruwa?” Kasa magana Baba yayi saida Ammi tamai ihu. “Baban Nanah!” Firgigit ya farka daga nisan tunanin dayayi ahankali yace “don’t worry I will handle everything gani nan zuwa” baijira mezata ce ba ya katse wayan daidai Aliyu na fitowa duk yay zufa ganin Baba shikadai tsaye a filin station din rana na dukanshi zufa na ketomai yasa yay wajenshi da sauri yace “Yallabai lafiya ka tsaya kai daya arana haka” juyowa yayi yakalli Aliyu, kafin anatse yace “come with me”.

✨SPARKLES OF AFFECTION ✨




     ✍🏻M SHAKUR

No comments