Gidan Aunty book 1 page 69-70

 


Page 69 





A rude Tahee ta dafe cikin ta , da wani irin shock take kallan Ammeey, kallo na tsantsan tsana , idan kowa yace zai ce Ammeey zata yi wannan abun bazata taba yadda ba sabida yadda ta nuna musu ‘kauna tun suna ‘kanana , bata gama shiga Rudu ba sai da taji muryar Ammeey ,” zaki yi tunanin ina sanku ko, toh babu Wanda na tsana a duniya kamar ku, sau dadama da na fara gina masarauta ta kune kuke ruguzamun, shiyasa nayi al’kawarin ruguza duk Wanda yayi ‘kokarin ta’bamun masarauta, bama ke ba koma wanene yayi gigin shiga gonata sai na kawar dashi. Ada nayi tunanin ‘kyaleki amma sam sai naga kin fu kowa za’kewa a cikin su wanda shine babban kuskuren da nayi na shigo dake cikin a halin nan,azato na baki da wayo,Aushe sam ba hakan bane , bana kawo ki gidan nan dan ki zauna cikinsu bane , na kawo kine dan ki ‘karasa aikin da na fara , na kawo kine ki kashe mun tahnoon , Wanda kike i’kirarun mijin ki a yanxu “. Cikin rud’ewa Tahee ta soma binta da idanuwa, gabaki d’aya jikinta rawa yake , jin maganganun ammeey take kamar a mafarki ko a cikin wani film da ba gaskiya ba ,”Ni na kashe mijina , bazai yuwa ba , mijina fa , kisa “, abunda Tahee take faman nanawa a cikin ranta . Ta sowa Ammey tayi daga kan kujerarta fuskarta babu ko alamun fara’a, Daidai inda Tahee take a zaune ta tsugunna itama tana bin fuskar Tahee da wani shu’umin murmushi,hannunta d’aya ta d’aga zata ta’bata Tahee tayi saurin bige mata hannu hawaye na sakkowa daga cikin idanuwanta, a zuciye Ammeey ta janyo kanta ba imani ta tsinkawa Tahee mari , cikin ‘kunar rai ta cigaba da magana “ idan kikai kuskuran musa mun abunda zansaki to ki tabbata yanda na kashe mahaifinki haka zan kashe mahaifiyarki da d’an uwanki, sannan na dawo kanki Keda abunda ke cikin ki da dole sai ya fita ko kina so ko ba’kyaso dan King nawane ni kadai, bazan ta’ba yadda wata taso abunda na dad’e inaso ba “. A zuciye Tahee take kallanta zuciyarta harwani tafarfasan ba’kin ciki take , cikin kunar rai ta d’aga hannunta da suke faman yi rawa tana nuna Ammeey, murya a sha’ke Tahee ta soma magana “ kece kika kashe mana Abbu dama, kece kika sa ayiwa Abbu yankan rago, duk tsawan wannan lokacin da sa hannunki a ‘batan Oumma da Taheer ?me mukai miki ?lefin me iyayena sukai miki da zaki sakamusu ta wannan hanyar?”mi’kewa tsaye Ammey tayi batare da ta damu da amsawa Tahee amso shin taba ,Wani ruwa da ta gani akan center din kujeran ta d’auta,cikin sakin murmushi ta soma magana “bani da lokacin amsa miki wannan tanbayoyin naki,amma kamar yadda nasha Alwashi , duk wanda yayi gigin tarwatsamun burukana toh kamar ya tarwatsa rayuwarsane, kamar yadda na salwartar da ran ubanki, na tarwatsa ahalinki, sannan na kashe miki d’an uwan mijin ki, na raba tsakanin uwa da d’a , bani da wani sai na cikar burukana da yayi saura yanxu kuma kece mukullun Karshen cikar burina , zan baki d’an kwanaki biyu , ki salwartar da abunda yace cikin ki sannan da ki kashe mijinki, idan ba haka ba ki fidda rai da kara ganin ahalinki har Abadah,”Tana kai karshen zancanta Ammey ta bar d’akin tana sakin wani shu’umin murmushi . “Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni karyan minha, Ya Allah kaga baiwarnan taka, Allah kai ne Wanda kace mu rokeka, Allah kaga wannan baiwa taka , Allah ka nuna ikonka akan bauwarka,” ta karasa zancanta tana sakin wani kukan bakin ciki, kukan da ta dad’e batayi irinsa ba , ace maka shin ka yana kusa da kai Wanda ka Amin ta dashi ka basa yadda yazamo shine makashinka, “Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un “,gabaki d’aya Tahee ta rasa Wana irin tunani zatayi sabida yanda komai na tunaninta ya tsaya mata , ji take komai da yake faruwa kamar a mafarki ne ba a zahiri ba , Wacce ta nuna masu so Itace maka shin mahaifinta , wani irin tsantsan tsanace taji tana yiwa Ammey da ya kore duk san da take mata , ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta lokaci guda , da kyar idanuwanta suke buduwata , a hankali ta lallaba ta nufi dakinta ko kallan gabanta batayi sosai , bata tsaya a ko ina ba sai kan gadonta, lokaci d’aya zazzabi da ciwon kai ya rufar mata daya sa wani irin bacci mara dadi ya d’auketa me cike da mafarkai.



***** 2:30pm ta farka daga baccin daya kwasheta tana karanto adduar da tazo bakinta , lokaci d’aya abunda ya faru d’azu ya shiga dawo mata cikin kwakwalwarta, tabbas d’an Adam butulune, sallahr azahar ta gabatar tana mika ka Allah kukan ta tare da adduar neman tsari daga Sharrin Ammeey da masu hali irin nata , a hankali kuma wasu zafafan hawaye suka shiga sakko mata cikin kwayar idanuwanta tuno irin yankan ragon da akai wa abbunsu, gashi bata san Wana hali oummanta suke ciki ba , a d’aya ‘bangaran kuma tana tsoran halin da mijinta zai shiga idan yasan wacece ta kashe masa d’an uwa , macen da ya d’auketa kamar mahaifiyarsa, macen da tafi mahaifiyarsa kusanci dashi , rana d’aya ya fuskanci Itace makiyarsa , “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un “,Na barki da Allah shi kadai yasan yanda zaiyi dake cewar Tahee tana goge hawayen fuskarta , a d’ayan ‘bangare na zuciyarta kuma ta sha alwashin sai ta tonawa Ammey a siri ko ta halin ‘ka’ka . Bata jin yunwa shiga bata yi abinci ba , sai ma addu’oi da ta du’kufa yi na Kariya a gareta da abunda yake cikinta . Yinin ranar gaba’ki d’aya cikin ‘kunar rai tayi shi , sai ma kokarin sassaita fuskarta da tayi gudun kar ya dawo yaga mood d’inta ya canza.


✨✨✨✨


Karfe 8:40pm king ya shigo part d’insa lokacin har Tahee ta kammala komai na ta ,ta saka wasu kayan bacci masu matu’kar d’aukar hankalin, gabaki d’aya kayan jikinta ana ganin surar jikinta,cikin wani irin salo ta karasa Wajansa tare da hugging d’insa , shi kansa king saida yayi ajiyar zuciya ga idanuwansa da ya fara canza kala zuwa kalar ja musamman yanda cikakkun breast d’inta suka ta’ba masa kirji, medium size jug d’in hannunsa yayi saurin dam’kewa , d’an d’age Tahee tayi kafun ta sakar masa peck a kumatunsa , cikin disashewar murya ya furta “ welcome back baby “, be amsa mata ba sai ma face d’inta da ya bi da kallo,” me yasa face d’inki tayi Jaa, are you okay ?” Saurin kawar da kanta gefe tayi tana kara saisaita face dinta , cikin yar shagwaba ta furta “ bakaine ka’ki dawowa ba , kuma babynka suna so su ganta , yaufa kamanta da mu gabaki d’aya ta ‘karasa kamar zata saka masa kukan shagwa’ba,”oh my god, zaki kasheni da wnnan salad naki ,okay dadyn baby yayi lefi ayi masa hakuri and anjima zamu gaisa da baby ai ko ?” Ya karasa yana kashe mata ido d’aya , kawar da zancan tayi ta hanyar karban karamin jug din hannunsa “ Menene wannan ?”, kallan jug d’in yayi kafun ya furta “ kunun aya Ammey tayi mun”, yana kai karshen maganarsa jug d’in na subucewa ya fad’i tass, gabaki d’aya ya tarwatse sai yar kwalbar da ta saukar wa Tahee a ‘kafa, kuka ta fashe masa dashi, cikin rud’ewa ya d’auketa yayi bedroom dinsa da ita , atunaninsa kwalbar data caketane amma ita sam ba haka bane , kukan bakin ciki ne yazo mata ganin saban Salan iskanci Ammey wato ta basu kunun aya su mutu.




#MANAGE PLEASE 🙏

GIDAN AUNTY

 

07041879581

  MSS LEE 💖



BOOK 1 


Page 70


Lallashinta yayi har tayi shiru bayan ya gama dressing din kwalbar da ya shigar mata kafa, wayansa ya dauka da niyar kiran Ammeey tayi saurin dakatar dashi ,bata san lokacin da bakinta ya furta me zaka mata, d’an kallanta yayi shima na ‘yan second kafun ya furta yaja hancinta kad’an “ wani kunun ayar zansa a kawo mana”, ita kanta bata san lokacin da take wani abun ba “ No kabari gobe zanyi maka wani kajiii babyn? Ynxu bari na fara temaka maka kayi wanka sai kaji abinci ,okay? Kanshi ya d’aga mata alamar toh kafun ya kuma cewa “ but bari na saka a kawo mana wani kunun aya , Kema ai naga kina san kunun Ammeey” no kaji ka fara yin wanka already na hada maka another juice please ni yunwa mukeji nida babyn ka fa “,cikin ya ta’ba kafun ya saki wani ajiyar zuciya “ toh ayiwa dady hakuri yanxu zakuci abinci” yana kai karshen maganar sa yashi ya nufi kofar da zata sadashi da ban dakinsu, ajiyar zuciya Tahee ta sauke cikin zuciyar ta kuwa cewa take “ Allah ya tsare na karacin abincin shaid’aniyar iblisarcan, Wanda naci a baya ma a rashin sani ne , muguwa me kama da kwarkwata, ta Allah ba taki ba “, gudun karya sakko ya tarar da abun kunun yasa tayi saurin fita daga d’akin, Daidai inda kunun ayar yake ta nufa , a bun mamaki amaimakon ta samu kunun ayar sai wani ‘bakin ruwa da ta samu, addua ta soma yi cikin xuciyarta, kafun taje ta dakko Mopper ma gabaki d’aya ruwan kunun ayar ya kuma komawa ba’ki , karfin adduarta ta soma tun tana yi a zuci haka ta cigaba dayii ita kanta bazatace ga adduar da take karantawa ba, da Bismillah ta fara goge ba’kin ruwan harta kammala, tare da kunna karatun alkurani yanda bazai damesu ba , tana cikin Kimtsa falon ya sakko ‘kasa shima cikin shigar kayan bacci blue colour masu Taushin gaske , serving Dinsu abincin tayi atare suke feeding din junansu har suka kammala , a kan 3sitter ya zauna ita kuma ta kwanta akan cinyarsa tana wasa da sajanshi “ babyn” ta kira sunansa a hankali kamar me rad’a , kallanta yayi alamar na’am duk da ne bud’e baki yayi magana ba “ wacece Ammey a wajan ka “ wani lallausan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa da ya kara kawata kyawun fuskarsa har hakan yaso bata mamaki, mi’kar da ita yayi zaune tare da kamo hannunta Suka nufi d’akinsa ta lipter , zaunar da ita yayi akan sofa kafun ya bar d’akin , mintuna kad’an kuma ya dawo hannunsa d’auke da wani karamin white box’s,budewa yayi take a wajan wasu hotunan Suka  bayyana duk da darewarsu amma babu abunda ya samesu,” sorry laifina ne da har yanxu baki gama sanin Tarihin mijinki ba,nasan kinsan full name dina , amma still zan kara fad’a TAHNOON ZAYED AL_NAHYAN, mumu 4 ummey ta haifa Akheee moha shine babba Allah ya masa rasuwa ,sai ukhtiii next tomorrow itama zaki ganta , sai ni sai kuma auta zoya , tun ina ‘karami na nake ‘bangaran Ammey sabida yanda take nunamun soyayya da wata shakuwa ta musamman komai ta samu ni zata fara bawa kafin ta bawa kowa na gidan har hakan ya kara sha’kuwa a tsakaninmu, soyayyar da take munne yasa sau da dama mutane sai su dunga d’aukar cewa ita tahaifeni sabida wani irin shakuwa da yake tsakanina da ita, part d’in ammeey na dawo cikin abinci, komai nawa a part din Ammeey nakeyinsa, hatta kwana a part d’in ammeey nake yi har lokacin tafiyata waje karatu, acan turkey na kammala karatun likitancina, har na kammala at time moment…” sai kuma yayi shiru yana runtsu idanuwansa , itama kallansa tayi sabida wani irin tausayinsa da ya mamayeta, tabbas ba karamin cutar dashi Ammeey tayi ba , hannunta d’aya ya dam’ke cikin nasa ,” At That moment, mukayi accident da Akhi , and at the same time motar da muke ciki ta kama da wuta , duk yanda nayi kokarin cecensa na kasa , ina jin zafin hakan every single day idan na tuna na kasa cetan best brother , I can’t save him, na kasa cetansa , agaban idona wuta ta ‘konashi” ya karasa zancansa kamar nunfashinsa zai d’auke , rungumeshi Tahee tayi tana fashewa da wani irin kukan tausayinsa , tabbas idan Ammeey zata iya ‘kona mutum da ransa toh tabbas zata iya yin kome tace ,a zuciyar ta kuwa fad’i take “Ammey kin cuci rayuwar mu, kin rusa mana farincikin , tana zan iya sanar Dashi kece kika kashe masa d’an uwa, kika rabasa da mahaifiyarsa”, shafa bayanta yake a hankali cikin rad’a rad’a ya furta “ banasan kukan nan naki idan ba so kike Nima nayi ba , duminki kawai nakeso,zuciyata ba dad’i inasan farin cikin matata “, ya karasa kalmar matata Tahee ta had’e bakinsu waje d’aya, duk yanda taso tsayar da hawayen fuskarta ta kasa , wani irin deep French kiss take basa, gabaki d’aya ta mantar dashi abunda ke damunsa, light din dakin king ya kashe kafun yaja bargo ya lullu’besu sabida sanyin da yake busosu…..



After 2 hours kwance take a jikinsa gabaki d’aya taki yarda su hada ido, “ a ina kika samo wannan karatun, I like it please kunyarnan ta tafi haka tana cutana fa “bugun kirjinsa tayi a hankali amma dukda haka saida yace ouuuush, yana kara rungumeta a jikinsa , lumshe idanuwanta tayi kamar me jin bacci Amma sam ba baccin take ba , tunanin yadda zata tona wa Ammey asiri kawai take a cikin ranta, tana cikin tunanin bacci ya d’auketa, forehead d’inta ya sumbata kafun ya ‘kara rungumeta a jikinsa, abubuwanda Suka faru tsawan shekarune suka dawo yawo akansa, babu inda ya fi tsaya masa arai kamar mutuwar d’an uwansa, ganin yanda jijiyoyinkansa suke ‘ko’karin ta shine yasa ya soma adduar tsari cikin zuciyarsa , ya d’ad’d’e yana addua kafun yayi nafila akan rokan Allah ya sassauta masa abun da yake ransa kafun shima ya kwanta yana kara rungumota a jikinsa.



********

✨✨✨✨✨


WASHE GARI king yana tafiya masallaci itama Tahee ta Tashi tayi sallarta, bacci take ji sosai shiyasa ta koma zata kwanta, a side d’in hagun da king ya fi kwanciya a gefen ta kwanta , hannunta d’aya ta zura ta karka shin pillow sa yanda zataji dad’in kwanciya sai taji abu kamar yana tokararta, gyara kwanciyar ta tayi yanda zata fi jin dad’in baccin nata amma still tanaji kamar abu na sukarta, ni’kewa zaune tahee tayi tare da yunkurin canza pillows din, hannunta ne ya sauka akan tsakiyar pillow d’in hannunta , da Sauri ta janye hannunta tana karantar addua, wajan ta kara ta’bawa amma still tanajin kamar akwai abu a wajan, cikin rashin tsoro ta kara kai hannunta wajan still har yanxu tana jin abinda takeji, rigar pillow d’in ta yi saurin zazzagewa kafun ta kara taba wajan, still dai abun na Wajan, cikin Sauri ta dauki pillow d’in ta nufi d’akin ta dashi, reza ta fara nema cikin sa’a kuwa ta samota, bakin pillown ta farka duka kafun ta zazzage abinda yake ciki, ‘karamar kwabace ba’ka ta bayyana a cikin abin cushion d’in, bakinta d’auke da Bismillah ta bud’e kwalbar, wani  haya’kine ya fito daga cikin kwalbar ba’ki’kirin da shi ,Addua Tahee ta fara da ‘karfi cikin ‘kan’kanin lokacin kuwa haya’kin ya bace gabaki d’aya . A Daidai lokacin da wannan kwalbar ta fad’o a daidai lokacin kan king yayi mugun sara masa , ga wani jiri jiri da ya soma d’aukarsa, part d’in ammey zaishi amma ya fasa ya nufi nashi part d’in, yana shiga cikin falon sa ya fad’i kasaaaaa..


#MANAGE

GIDAN AUNTY 

07041879581

MSS LEE 💖


MAI BUKATAR KARANTA GIDAN AUNTY HAR KARSHE YA TUNTUBENI TA NUMBER TA .


BOOK 1

No comments