Furar Danko Book 2 Page 9

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻






𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣



........Dariya sosai Alhajin ya kwashe da shi. “Karka damu da sanin ni wanene saboda nasan kai waye? Sanin aikin da zakai min kawai ne yafi muhimmanci. Dan na sanka fiye da yanda na faɗa maka a yanzu. Kaɗan na tsinkulo a sanin danai maka kawai. Gidan daka ajiye aiki nake so ka koma ka cigaba da min aiki. Duk wata zan baka albashin naira dubu hamsin bayan albashin da su suke baka dubu ashirin”. Ya ajiye masa wani envelope gabansa da cigaba da faɗin, “Wannan shine kundin ayyukan da zakamin a gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi. Zan iya baka dama ta kwana ɗaya kaje kayi tunani, sai dai ka sani ko'a cikin ɗakinka idanuna a kanka suke, dan haka da zuciyarka kawai nake buƙatar kayi nazari. A duk sanda nake buƙatar magana da kai zan nemeka tanan” ya ajiye masa waya akan envelope ɗin daya ajiye gabansa. “A yanzu bana buƙatar cewarka anan, kaje kayi nazarin na barka lafiya. Ku maidashi”. Ya ƙare maganar da duban yaransa cikin bada umarni

       Da wani irin kallo mai nuna tsananin zafin zuciya Uncle Smart ya bisa. Sai dai da alama ran ƴan maza ya ɓaci dan ya kasa furata komai.....


        Kamar yanda Alhajin ya bada umarni sun maidoshi har kan titin anguwarsu. Kasancewar magrib yayi a gurguje ya ƙarasa gida domin watsama jikinsa da yay nauyi ruwa. Ya samu wasu daga cikin samarin ƙannensa sun dawo gidan. Wanda ya samu a waje suka gaishesa. Da hannu ya amsa musu kawai ya shige ɗakinsa. Shi mutum ne mai tsafta sosai da ƙwanƙonin tsiya, dan haka ganin ɗakin a yanda ya barsa ya sashi jan tsuki yana ɗan dafe kansa dake masa ciwo. Har yanzu abinda suka shaƙa masa bai gama sakin masa jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa, cikin sa'a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur'ani kiran ya shigo, cike da zumuɗi Asma'u da wayar ke'a gefenta ta ce, “Lah Yaya ne”. Kallonta Ammi da Maryam ɗin duk sukayi, ita kuma ta ɗaga da sallama. A hankali ya amsa mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da faɗin, “Zan samu ruwan zafi a wajenku?”.

       “Eh Yaya”.

Ta amsa masa cike da girmamawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, “Ya dawo ne?”. Kai ta ɗaga mata da faɗin, “Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyi”. A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke'a tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baƙar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan ƴaƴanta idan yana faɗa haka yanzu ma ta haɗiye, sai da ya gama ta bashi haƙuri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuƙar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana ɗaki amma suka samu baya nan ɗakin ma a buɗe, neman number sa ta shiga yi amma sai ba'a ɗaga ba, daga ƙarshe ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma'un. 

        Koda Asma'u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga, ɗakin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar magriba yay tashi a ɗaki sannan ya fice massalaci yin isha'i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk ɗakunan matan gidan ya gaidasu. Da ɗakin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai yawan fara'a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa'anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda ƙaramar tazo jikinsa tana kawo masa ƙarar ɗan uwanta dake bima babbar ɗakin nasu cewar ya karya mata pencil ɗinta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, “Yayanmu ƙarya take ita ta karya abunta a makaranta suna faɗa da Ameer. Kuka ta saka itama tana faɗin, “Ƙaryane Yaya shine”. Hannu ya ɗaga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, “Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun ɗazu suke rikicin nan ni harna gaji ma da magana”. 

      Faɗa yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo ɗakinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa ɗakin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan ƴaƴa a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran ƴammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a ɗan fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba autarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miƙewa. Dakatar da shi Umman tayi da faɗin, “Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?”.

    Ɗan murmushin ƙarfin hali yay mata da faɗin. “Ba komai Umma na fitane da safe sosai wani uziri”.

     “Uhhm to yayi”. Ta faɗa a taƙaice.

     Iska ya ɗan furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa ɗanta na huɗu kawai ya samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur ɗin yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya. 

      “Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kanka”. Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana ƙunƙuni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da ƙarfi.


      Ammah na zaune su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa abinci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da ɗauke kai ta ce, “Lafiya ka fita tunda safe?”.

       Samun kansa yay da faɗin, “Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne”.

        A hankali ta sauke numfashi. “Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka karɓi rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowane bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar ɗawainiya da ku tun kuna ƙanana har girmanku, bai tauye kowannenku ga ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe idanunmu”.

        Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gyaɗa kai da tausasa harshe ya ce, “Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu'a”.

    “Addu'a kullum cikin yimuku muke babu fashi”.

    Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da yay shafa'i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope ɗin nan ya ɗakko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa ɗauke da rubutu mai ɗan tsaho, abubuwan da aka rubuta ɗin ya matuƙar bashi mamaki harma ya rasa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya faɗa to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Takardar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci......


    _______________________★


        Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa akan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf ɗin ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za'a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kansu. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf ɗin yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya ɗaga mata ya ɗauke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?. 

      “A'a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy.....”

    Bata gama rufe baki ba sai gashi ya fito kamar a ɗan rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya buɗe masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart ɗin shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya ɗakkoma key yay masa sallama. Juyowa yay ya ɗan kallesa, har ya ɗauke kai sai kuma ya sake jiyowa. 

      “Alhamdullah” ya faɗa yana miƙo masa key ɗin batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key ɗin, dannawa yay motar tai ƙara, dan haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya buɗe masa yaga ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin, “Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ruɗewa irin haka ba ƙarami bane ba”.

         Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba ɗaya ba.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

No comments