Furar Danko Book 2 Page 14
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣
.......“Look Olivia, kin san dai zan iya aikata miki komi ko? Ciki harda datse jijiyar numfashinki. Kin sanni na sanki ciki da bai, ki faɗa min yanda akai ciki bai fitaba?”.
“Mi kake so na sanar maka bayan wanda na faɗa?, Na faɗa maka iya abinda na sani ai, kasan irin haɗarin dana saka kaina wajen maka yanda kake so bayan kauce ƙa'idar allurar daya kamata nai mata. Kaifa ka kawo allurar nan kuma na cika umarninka nai mata, a gabanka komai ya faru kuma ko balle kace na yaudare ka”.
“Ƙarya kike Olivia, sai dai idan fakar idona kikai kika canja allurar dana baki. Dan babu macen da aka taɓa gwada wannan allurar a kanta hakan ta kasance kema kin sani. Sannan ƙarya kike bakuyi mata wankin ciki ba”.
Shiru tai kamar bazatace komai ba, sai hucin ɓacin rai takeyi kamar yanda shima yake yi. Wayar landline ta jawo tai kira, kai tsaye ta bada umarnin a sameta a Office. Mintuna baifi uku ba wani nurse baƙin fata ya shigo. Cikin girmamawa yayma Dr Olivia barka da shigowa tare da ɗagama Alh. Sulaiman hannu a taƙaice. Dr Olivia ta dubesa bayan ta zaro wani file a gefenta ta miƙa masa. Amsa yay cikin rashin sanin mizaiyi da shi.
Ta ce, “Buɗe”.
Babu musu ya buɗe tare da ɗan duddubawa, sai kuma ya ɗago yana kallon doctor. Kafin yace wani abu ta tareshi da faɗin, “Ban sakaka yima mai wannan file ɗin wankin ciki ba a ranar data samu miscarriage?”.
Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya dubeta yana cewa, “Ƙwarai anyi haka doctor, sai dai kuma an samu akasi ai a ranar bamuyi mata ba saboda yanayin mahaifarta mukace bayan kwana biyu su dawo sannan ta huta saboda sun matsa a sallameta....”
A zafafe Alh. Sulaiman ya yunƙuro zaiyi magana Dr Olivia ta girgiza masa kanta. Ita ta ƙara fuskantar Nurse ɗin da faɗin, “Amma miyasa baka sanar min ba? Sannan da baki ka faɗa musu ko'a rubuce?”.
Kai tsaye yace, “Nazo sanar miki sai na samu kin fita. A rubuce kuma muka basu gaskiya, kuma ita muka bamawa ma a hannunta ai”.
“Okay zaka iya tafiya”.
Ɗan rissinawar girmamawa yay tare da ajiye mata file ɗin ya fice. Yana rufe ƙofar ya saki murmushin mugunta, a zuciyarsa yace (Ƴan iska ai dama nayi alƙawarin saina kuɓutar da yarinyar nan. Wankin ciki kuma ina kan sani naƙi yinsa bayan nai mata allurar tsaida jini da sauri ta yanda cikin bazai fita ba. Ina Musulmi baƙar fata bazan taɓa bari a cutar da wani musulmi ba in sha ALLAHU in dai ina asibitin nan. Tunda har naji hirarku dama nai alƙawarin taimaka mata dan na fahimci zaku cutar da ita ne bada saninta ba).
A ciki kuwa shiru Office ɗin ya ɗauka. Da ga Alh. Sulaiman har Dr Olivia kowa ya kasa cewa komai. Sai can ta nisa da ƙyar ta katse shirun da faɗin, “Yanzu ka yarda na maka aikinka ko? Sannan babu kuskurena a ciki na turata inda za'a mata wankin ciki, kaga kuma sun basu damar su dawo amma baku dawo ba, hakan na nufin yarinyar bata son rasa cikinne ko wani dalili daban.....”
Cikin wani irin baƙin ciki da zafin zuciya Alh. Sulaiman ya furta, “Dalilinta na banza. Ciki kuma dolene a zubar da shi”.
“Gaskiya bazai yiwu ba, inba haka ba kuwa komai zai iya faruwa kamar yanda na faɗama Mrs Garko. Ciki kuwa harda rasa ranta. Ni kuma bazan iya gangancin aikata haka ba a wannan gaɓar dan zai zama taka doka, cikin wata biyar da kusan sati biyu, taɓashi da niyyar zubarwa ai kowama yasan ganganci ne. Kawai ku barta ta haihu tunda tana son abinta”.
“Ashe zan kashe yarinyar nan kuwa!!” Alh. Sulaiman ya faɗa a wani irin kausashe jikinsa har ƙyarma yakeyi. Ita Dr Olivia ma duk sai tsoro ya kamata. Nurse ɗin nan ne yay knocking ƙofar ya shigo, cikin girmamawa ya aje wani file a gaban Dr Olivia a yanayin dafa tebirinta, hakan ya bashi damar zare ƙaramar wayar da ya ajiye batare da sun lura ba saboda rufewa da idanunsu sukayi. Daga haka yay ficewarsa yana ɗan murmushi....
Fitarsa kusan da mintuna biyar sai ga Alh. Sulaiman ya fito ransa a matuƙar ɓace tamkar zai kifa a cikin sassarfa. Nurse ɗin nan yay murmushi da biyo bayansa da sauri-sauri. Sun ɗan yi nisa a doguwar barandar yaji kamar ana binsa a baya. Jiyowa yay cikin sauri sai sukai arba da Nurse ɗin nan. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru sakamakon tare numfashinsa da Nurse ɗin yay cikin harshen Hausa. Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Alh. Sulaiman, duk da kuwa hakan ba wani abun ai mamakin bane kasancewar matashin saurayin baƙin fata. Amma gaskiya bai tsammanin jin Hausa a bakinsa ba. “Sunana Usman B Sa'eed. Bahaushe haihuwar Nigeria girman Canada. Na biyoka ne nan saboda jin ina son taimakonka matsayin ƙabilata kuma addinina.”
Kamar Alh. Sulaiman zai yaɓa masa magana sai kuma dai ya haɗiye, yaga ya kamata yaji ƙarshen zancen. Usman ya cigaba da faɗin, “Dr Olivia bazata baka haɗin kai ba dama, dan kasan turawan nan da son bin ƙa'idar abu. Sannan gaskiya ta faɗa in har ta aikata sake zubda cikin aka samu matsala to akwai babbar ƙura da ku kanku zata iya shafarku. Karka manta anan sun san hakkin ɗan adam ba irin yankuna mu na Africa bane ba da zaka iya yin komai ba komai. Na fahimci cikin irin wanda mu mutanen Hausawa muke gudune wato na shege shiyyasa kuka matsu ku zubar. Dan haka zan taimaka muku ta yanda zaku salwantar da shi cikin sauƙi batare da kowa ya fahimta ba. Sai dai zai kai haihuwa, amma za'a haifesa ba'a raye ba, dan zan dinga mata allurar da yaron zaita ruɓewa a cikin nata batare da an fargaba itama kanta bazata fahimta ba dan na gane bata so a zubar da shi shiyyasa taƙi dawowa wankin ciki”.
Sosai Daddy yake nazartarsa, amma abin mamaki ya kasa hango yaudara a tattare da shi. Dan Usman irin mutanen nan ne masu maida abu serious ka kasa fahimtar gabansu da bayansu. Kai Daddy ya ɗan jinjina kawai tare da miƙa masa hannu. “Zan iya baka number ka sameni a gida bayan nayi shawara”.
“A babu damuwa ai Alhaji”. Cewar Usman cikin dakewa. A zuciyarsa kam sai dannama Alh. Sulaiman zagi yake kala-kala. Dan yana ayyana sune masu fita ƙasashen waje suna zubar mana da mutunci ana kallonmu wawaye creminal. Ya bashi number wayan suka rabu, da ga haka ya fice a asibiti ya samu taxi ya shiga dan anan baida lasisin tuƙi. Maimakon gida sai ya nufi can wani joint a bayan gari kaɗan, wajene na sheƙe aya matuƙa dan mata na yawo ne babu sutura. A can ya samu ya huta zuciyarsa ta huce da samun damar yin tunani akan Usman Nurse. Ya fahimci wannan ita kaɗaice mafita kam a garesa. Dan yana son tabbas shegen cikin nan ya zube saboda shine sharar fage na farko da yake son ƙuntata rayuwar Smart da ita. Kafin ya tafi matakin farko akan Daddy da Smart ɗin harma da Uncle Yousuf, dan akan Lulu yake son ya musu tarko su ukun ta yadda zasu koma su kansu basu yarda da kansu ba. Wannan shine sabon plan ɗin da ya canja akan kowanne su. Tajuddeen kuwa lokaci yayi da zai kaɗa kansa ya bar Canada. Dan ya gama masa aikin da yake so, dama amfani kawai yake da yaron nasa a matakin dalillai biyu. Na farko manufarsa tun fil azal. Na biyu halin ciwo da yake ciki akan yarinyar shiyyasa yake biye masa kamar gaske dan ya samu kwanciyar hankalinsa. Dan gaskiya yana ƙaunar yaron fiye da sauran ƴaƴansa. Saboda kasancewar sa namiji ɗaya tilo a cikinsu. Yana ganin bayan ya tsigesa mataki na biyu da zaibi a kansa shine bin shawarar amaryarsa akan haɗashi aure da ƙanwarta, dan ya gamsu da bayanin datai masa ya kuma ɗauki shawararta. Sannan ita kanta Dada lokacin gama nata aikin yayi.
Koda ya koma gidan sai bai cewa Dada komai ba koda ta tambayesa ya batun zuwa asibiti. Sai da ta ƙara maimaita masane ya ce ta saurareshi yana nazari ne. Badan Dada taso ba dole tai shiru ganin ya haɗe fuska. Ummita dake laɓe tana jinsu, sai dai bata so jin Alh. Sulaiman yay shiru ba. A lokacin da duk wannan cakwakiya ke faruwa Smart na can cikin farin cikin samun nasarar cin ƙwallon da sukai tsakaninsu da abokan hamayyarsu ƴan Model Unitet a wannan ranar......
Bayan kwanaki biyu Alh. Sulaiman ya kammala yanke hukunci akan zancen Usman Nurse, sai dai bai nemesa ba sai da ya saka akai masa bincike a kansa tsaf. Inda aka kawo masa bayanai akan tabbatar da cewar karatu ne ya kawo mahaifinsa ƙasar Canada, amma asalinsu ƴan Nigeria ne. Anan Usman ya girma dan yana da shekara kusan goma iyayen nasa suka dawo Canada, sai dai fa yana yawan zuwa ƙasar haihuwar tasa. Usman dai a zahirance baya jin magana sam, dan duk wani ɗani'u na turawan nan yana zubasu musamman neman mata, kuma kamar yanda yake a turai hakan ba komai ba suma iyayensa basu ɗauke sa komai ba. Bai taɓa aure ba amma yanada ilimi mai dan babban Nurse ne shi ɗin. Wannan bayanai sun ƙawatar da Alh. Sulaiman, dan ya nazarcesu tsaf da fahimtar su a yanda makauniyar zuciyarsa ta tabbatar masa. Abinda bai sani ba Usman yarone mai matsanancin kishin ƙasarsa da ma yankinsa na Africa har ma da addininsa duk da waɗan nan rashin jin nashi. Wannan aƙidar tasa tasa ko kullum yake cikin yawo tsakanin Nigeria Da Canada kamar wani ɗan sama jannati. Dan ko aikin ma anan da ƙyar mahaifiyarsa ta samu ya yarda yakeyi, amma duk da haka sai da yaje ainahin ƙauyensu ya buɗe wani ƙwarya-ƙwaryan asibiti ya zuba likitoci da ke aiki a cikin kuɗi ƙalilan wa marasa lafiya. Koda Alh. Sulaiman ya gama tattare abinda yake buƙata sai yay ma Dada wayo akan ta koma wajen Baba, ciki Lulu kuwa su barshi ta haifi abinta kawai tunda dai Dr Olivia ta tabbatar musu akwai matsala. Ba haka Dada taso ba, sai dai bata iyayima ɗan nata musu, ganin kuma ya dawo da passport ɗin Lulun da Ummita ya basu ya sakata jin kwanciyar hankali, dan haka badan taso ba ta shirya ta koma wajen mijinta da al'amarin nata ya sashi fara tsarguwa shima. Sai dai baice mata komai ba tunda ta ce masa wasu kaya zata duba a Canada ɗin dama kafin ta wuce........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments