Furar Danko Book 02 Page 16

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗.





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣




.......Tun a randa suka fara fitowa Lulu ta fahimci zagaye suke da idon yaran Alh. Sulaiman, amma maimakon ta razana sai ma tayi murmushi. Batace da tacema Ummita komai ba akan hakan, sai ma zunguran Ummita data shigayi game da sanin wacece ita? Da yanda akayi ta yarda ta biyosu Canada. Tuni hawaye suka cika idon Ummita. Bata hanasu zuba ba sannan bata sharesu ba, sai da ta jiƙe gaban rigarta sosai kafin cikin shashshekar kuka ta ce, “Sunana na yanka Fatima. Naci sunan kakata ne shiyyasa ake kirana Ummita. Asalinmu ƴan wani garine ɓagwai a ƙauyen bichi. Anan nai karatun primary ɗina, da ga baya aka kaini boarding school a wata makaranta da ake kira GGASS Ɗan/zabuwa. Naje har js 3 aka cireni na koma cikin garin Kano hannun yayata da ke aure acan sakamakon rashin lafiya data kwanta. Jeka ka dawo na koma zuwa ina kula da yayata a gidan mijinta tsahon shekara biyu harta fara samun lafiya. Tun ban wuce shekara ɗaya a gidan ba mijin yayata ke nunamin wasu abubuwan rashin ɗa'a, sai dai bana kulashi sai da naga abin na neman wuce gona da iri na nuna inason komawa gida dan ban son faɗama yayata na tayar mata da hankali. Amma sai iyayenmu sukaƙi yarda yayar tawa ma harda kukanta, acewarta idan na tafi wazai ringa kulawa da ita da ƴaƴanta biyu kamar ni. Tausayinta ya kamani sosai, dan haka na haƙura na zauna, sai dai na ɗauki matakan kare kaina tako ina har takai mijin nata shima ya daina shiga sabgata ya kama kansa. Ashe lumbu-lumbu yay min, dan sai da ya bari na shagala sannan a wani dare ina gab da kammala ss3 ya bankama yayar tawa maganin barci ya keta mun mutuncina. Maganin daya banka mata yay sanadin barinta duniya, na shiga tashin hankali irin wanda baida misali, sai dai na gagara faɗama kowa asalin al'amarin har akai sadakan uku. Ina murna zan koma gida sai babana yace na zauna tare da gwaggonmu mu kula da yaran harna ƙarasa jarabawar neco da waec da zamu fara. Naso tada hankalina amma akaita tausata, ganin akwai gwaggonmu ya sani jin zan daure ɗin. Mun fara jarabawa ina a cikin yanayin rashin jin daɗin jikina. Haka dai naita daurewa yayinda iyayenmu a bayan fage batare da sanina ba suke shirye-shiryen aurar da ni wa mijin yayata matsayin madadi waina riƙe yaranta. Da farko ya yarda sai dai a randa muka gama jarabawar ƙarshe na kaita a wahalce, tun daga makaranta aka wuce dani asibiti, inda a gwajin farko aka sanarma gwaggona da tazo inada shigar cikin wata biyu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, babu bin ba'asi babana ya hau dukana Sakamakon zugar da mijin yayata yay masa akan dama ance ina yawon banza ai, baya son ya faɗa ne ace dan karya auranne yake son zamewa. Iya jijjiga kamalamansa sun jijjigani, yayinda ɓacin rai ya saka baba rantsewa bazan zauna masa a gida ba. Hankalin mahaifiyata ya tashi, amma sanin halin mahaifinmu ya hanata cewa komai, sai shawarar turani Abuja data yanke wajen ƙaninta. Matar ƙanin mamana na samu damar warwarewa komai da ya faru, ranta ya ɓaci matuƙa ita da ƙanin mamana, dan haka suka ɗaukeni muka juya Kano suka shigar da ƙara kotu tare da neman lawyer daya san aikinsa sai aka haɗamu da ke. A lokacin baki jima da dawowa Nigeria ba kamar yanda naji ance, dan hausanki ma ba wani sosai yake fita ba. Kin taka rawar gani a rayuwata ta hanyar tabbatarma mijin yayana MACE MUTUM ce (Rahma Abdull-majeed. Wanda bai karanta littafin nan ba wlhy anyi bashi🥱). Dan sai da kika turashi gidan yari har yanzu kuma yana can. Uncle ɗina bai saurari iyayena ba da suka shiga nadama sosai ya ɗakkoni muka sake dawowa Abuja. Inda ya nema min makaranta na fara. Ga rainon ciki inayi, cikin danai matuƙar tsana a rayuwata har ALLAH ya kaini ranar haihuwa. Sai dai alhmdllh jariri baizo da rai ba. Hakanne ya sani farin ciki na maida hankali a karatuna. Bana zuwa gida saboda gudun zunɗen mutanen ƙauye harna kammala karatu na na samu result mai ƙyau, ina cikin neman aiki ne sai ga Hajiya Shuwa a gidan mu kasancewar tana huɗɗa da aunty na, tana kawo mata turaren wuta. Jin ina neman aikin taimin tayin wannan aikin, sai dai tace aikin na shekara ɗaya ne kacal shiyyasa kawuna ya amince da sauri, ni dai bance komai ba dan banjin zanje ɗin, sai a randa na ganki matsayin wadda za'aima aikinne ya sani yarda da sauri-sauri domin rama alkairi da kikai min nima....”

       Tuni hawaye sun jiƙe fuskar Lulu, jik 10inta har wani tsuma yake kamar wadda ake kaɗama gangi. Lura da hakan ne yasa Ummita kamata suka koma ciki batare da ma lokacin da aka basun ya cika ba.....

          

      _________★


   A ɓangaren Dada tun a washe garin da Alh. Sulaiman yasa aka canjama su Lulu wajen zama yay kiranta cikin tashin hankali da makirci yake sanar mata baiga su Lulu ba, yazo gida ya samu sun gudu. Yasa ƴan sanda nemansu da ga baya suka fahimci sun bar ƙasar ne da taimakon wani dan har note aka bar masa. Hankalin Dada yay masifar tashi har takai ta kasa controlling kanta Baba Garko ya fahimta. Tambaya ya shiga jera mata wadda ta kaita da gaya masa cewar Lulu ta gudu da ga Canada, kuma suna zargin wani ne ya sace ta. Cikin matuƙar mamaki Baba Garko ya ce, “Canada kuma Hajarah, miya kai Mawaddat Canada ko ita da mijin nata ne?”. Wannan kalma ta Baba ce ta dawo da Dada a hayyacinta. Duk kuma sai ta daburce ta rasa abin cewa  har takai Baba Garko ya daka mata tsawa, tasan halinsa baya ɗaukar raini, idan ya juye mata takan rasa gane kansa, kafin yay hakanne akan jima shiyyasa take samun damar iskancinta. Waya ya ɗauka ganin bazata bashi gamsashiyar amsar da yake buƙata ba yay kiran Daddy. Sai dai wayarsa taƙi shiga, yasan hakan nada nasaba ne da yanayin network. Ganin zancen waya ma bazai bashi yanda yake buƙata ba a ranar ya saka autansa namiji da tunda yazo da iyalinsa bai koma Saudiyya inda yake aiki ba ya yanka musu ticket, dan yace yau bazai sake kwana a ko'ina ba sai a Nigeria, saboda ya fahim al'amarin babba ne. Hankalin Dada ya sake tashi, amma tasan a wannan gaɓar bata isa yi masa wani daɗin baki ya dakata ba, dole ta shirya suka wuce a tare. 

      Sunma Nigeria ƙasar haihuwarsu saukar dare, hakan sai ya sirranta dawowar tasu suka samu damar isa gida cikin kwanciyar hankali. Kowa ka gani a gidan Baba Garko ma'aikata cikin farin ciki yake da samun lafiyar tsohon abin son kowa. Mai tausayi da son ƙyautata rayuwar na ƙasa da shi, mai jan ɗan aiki jikinsa tamkar ɗan uwa ba bawa ba. Bayan albashinsu da ba'a taɓa tauyewa ba a koda yaushe cikin musu alkairin yake. Ko Zakka ya fitar sukan samu kaso mafi tsoka duk da Dada bata son hakan. Sannan duk abinda ya samu iyalansu ko lafiyar jikinsu yakance su sanar masa dan shine da hakkin wannan. Wannan yasa su jin ƙaunarshi da shiga a tashin hankali a duk lokacin da suka ga yana a cikin damuwa ko farin ciki. Sam hankalin Dada baya a jikinta, suna isowa sashenta ta wuce, layinta na Nigeria ta ɗora a waya sai dai kafin ya gama dai-daita duk ta ƙosa, hakan ya sata amsar wayar mai aikinta domin kiran Daddy. Amma abin mamaki sai ta samu number busy, bata kawo a ranta da mijinta Daddy ɗin ke kiran ba, dan haka ta cigaba da jera masa kira. Shiko Daddy dake waya da Baba Garko ganin baƙuwar lamba ce yasa koda ya kammala bai ɗaga ba, ganin ma za'a damesa ya sashi saka wayar a airplane mode kawai. Haukane kawai Dada batayi ba a wannan dare jin daga baya ma ta daina samun Daddy ɗin. Karo na farko da taji takaicin rashin riƙe number kowa na jikinsa da ga shi sai Lulu. Dan ko Yousuf ita bata da lambarsa. Matarsa kuwa (Mommy) dama ba huɗɗa take da su ba. Barcin kirki dai Dada bata sameshi a wannan daren ba sam. Tana sallame sallar asuba sai kuma ta fara jerama Daddy kira, sai dai har lokacin wayar bata shiga. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kuma kasa zuwa inda Baba Garko yake. Dan gani take kamar yana riga ya gama jin komai da komai. Tayi kiran Sulaiman kuma shima wayarsa bata shiga ba sam...


     A ɓangaren Baba Garko ya gama fahimtar akwai matsala, sannan koma minene akwai saka hannun matar tasa a ciki. Yay kiran Daddy kuma dan yaji gaskiyar zance game da zuwan Lulu Canada sai ya samu numbersa busy. Akan Uncle Yousuf ya maida akalar kiran nashi, inda yaji komai da komai, yana gama wayar da Uncle Yousuf ɗin ne kuma kiran Daddy ya shigo masa. Maimakon ya tambayesa kamar yanda ya tambayi Uncle Yousuf sai ya canja kawai suka gaisa ya sanar masa yazo Nigeria, yana son da safe ya samesa a gida da wuri. Daddy yayi farin cikin jin Baba ya samu lafiya, sai dai ya shiga mamakin jin kiran gaggawa da yake masa. Wanda yasan koda bai kirashi ba tunda yaji ya dawo ƙasar da safen dole zaije gidan duba shi.

          Zuwa ƙarfe bakwai da rabi duk wanda Baba Garko ya buƙaci gani a gidan nasa ya iso. Dan harda ƴaƴansu ƙannen Alh. Sulaiman ɗin. Uncle Khamil da auta da suke kira Uncle Sadiq ne kawai babu dan shi sun barosa acan, sai kuma Alh. Sulaiman da shima dai fushin da Baba keyi da shi yasa bai saka shi a cikin meeting ɗin gaggawar ba. Sosai kowa ke cikin farin ciki da ganin yanda mahaifin nasu ya samu lafiya kamar bashi ba. Zamansu babu jimawa ƴan sandan dake bincike akan case ɗin sa suka iso gidan. Ya ce suyi haƙuri suje zuwa anjima zai nemesu yanzu yanada muhimmin uziri ne da iyalansa.......✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments